Kotu ta kori bukatar DSS na neman ci gaba da tsare Emefiele

Babbar Kotun Abuja ta yi watsi da bukatar hukumar DSS da cewa ya saba tsarin kotu

Kotu ta kori bukatar DSS na neman ci gaba da tsare Emefiele

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar da hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta shigar a gabanta neman izinin ci gaba da tsare dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele na karin kwana 14 bayan kotu ta ba da belin sa.

A ranar Talata DSS ta shigar ta karar ne inda ta shaida wa kotun cewa tans bukatar ci gaba da tsare Mista Emefiele saboda ta samu Karin hujjoji kan zargin da take masa.

Hukumar ta yi hakan ne bayan caccakar da ta sha kan yadda jami’anta suka yi wa takwarorinsu na hukumar gidan yari karfa-karfa wajen sake tsare Emefiele a harabar Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Legas, wadda ta ba da belinsa a ranar Talata.

A yayin sauraron sabon karar da DSS ta shigar, Mai shari’a Hamza Mu’azu na Babbar Kotun Abuja, ya yi watsi da bukatar hukumar da cewa ta saba tsarin kotu, domin kotun ba ta da hurumin sauraron bukatar.

Da ya tambayi lauyan hukumar, Victor Ejelonu, ko ba kotun Majistare ke da hurumin ba da izinin tsarewa ba, sai lauyan ya janye karar.

DSS ta sake tsare Emefiele bayan dambe da jami’an gidan yari

Kotun da ke Legas ta ba da belin Emefiele ne bayan ya musanta zargin da hukumar take masa na mallakar haramtattun makamai, ta kuma ba da umarnin shi a gidan yari, zuwa lokacin da zai cika sharuddan beli.

Kotun ta shardanta biyan Naira miliyan 20 da kuma jami’an gwamnati da suka kai matakin aiki na 16, wadanda kuma za su mika fasfo dinsu.

Sai dai a yayin a jami’an hukumar  gidan yari ke shirin tafiya da shi kafin cika sharudan belin ne jami’an DSS suka zo da nufin sake tsare shi, lamarin da ya kai ga tayar da jijiyar wuya a tsakanin bangarorin, wanda a karshe jami’an na DSS suka murkushe jami’an gidan yarin suka yi awon gaba da shi.

Wannan lamari dai ya jaw a hukumar Allah-wadai daga Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) da sauran ’yan kasar.

Daga bisani hukumar ta fitar da sanarwa tana nesanta kanta da abin da jami’an nata suka aikata, da cewa za ta gudanar da bincike domin hukunta wadanda ta samu da laifi.

Tsakanin DSS da Emefiele

Kawo yanzu Mista Emefiele ya shafe kwana 47 a hannunta bayan da ta tsare shi a ranar 10 ga watan Yuni, washegarin da Shugaba Tinubu ya dakatar da shi daga aiki.

Hukumar ta shigar da karar Mista Emefiele a karfon farko ne bayan da ya kwana 35 a hannunta, bayan da kotu ta umarce da ta aikata hakan ko kuma ta sake shi.

DSS ta tsare shi ne bisa zargin ta’addanci, amma daga bisani ta gurfanar da shi a kan zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, lamarin da wasu ’yan kasar suka yi ta ce-ce-ku-ce a kai.

Tuni dai ya musanta zargin, tare da kalubalantar hukumar ta kawo hujjojin da ke tabbatar da zargin.

A karshe dai kotun ta ba da belinsa, amma kafin tafiya da shi gidan yarin Legas, kafin ya cika sharuddan belin ne jami’an DSS suka yi dambe da jami’an gidan yarin suka kwace shi daga hannunsu.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta