Kotu ta kori dan takarar Gwamnan Kano na PDP
Babbar kotun da ke Jihar Kano ta kori dan takarar Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar adawa ta PDP, daga cikin sauran ‘yan takarar Gwamnan da za a yi ranar Asabar mai zuwa. Kabir shi ne dan takarar da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya tsayar a matsayin dan takarar Gwamnan jihar na jam’iyyar […]
Babbar kotun da ke Jihar Kano ta kori dan takarar Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar adawa ta PDP, daga cikin sauran ‘yan takarar Gwamnan da za a yi ranar Asabar mai zuwa.
Kabir shi ne dan takarar da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya tsayar a matsayin dan takarar Gwamnan jihar na jam’iyyar PDP.
Mai shari’a na kotun Lowis Allagoa ya bukaci jam’iyyar da ta gudanar zaben fidda gwani daga yau zuwa ranar 9 ga Maris 2019.