Kotu ta kori Gabriel Suswam a matsayin Sanatan Benuwe 

Kotun ta ce hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta zartar akwai kuskure.

Kotu ta kori Gabriel Suswam a matsayin Sanatan Benuwe 

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, ta kori tsohon gwamnan Jihar Benuwe, Gabriel Suswam daga Majalisar Dattawa.

Kotun a wani mataki na bai daya da wasu alkalai uku suka yanke a ranar Laraba, ta ce ta gamsu da cewa Suswam ba shi ne ya lashe zaben Sanatan Benuwe ta Arewa Maso Gabas a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kotun ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben Jihar Benuwe, wadda ta tabbatar da Suswam na jam’iyyar PDP a matsayin Sanata, bayan ta soke nasarar Mista Emmanuel Udende na jam’iyyar APC.

A cewar kotun daukaka karar, an yi kuskure a hukuncin baya wajen tantance shaidun da jam’iyyun suka gabatar a gabanta.

Don haka, kotun ta yi watsi da hukuncin kotun, inda ta ce karar da dan takarar APC ya shigar a gabanta ta cancanta.

“Kotun sauraron kararrakin ta yanke hukunci a zabe ranar 8 ga watan Satumba, 2023.

“An dawo da wanda ya shigar da kara a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Benuwe ta Arewa maso Gabas da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.”

Idan dai ba a manta ba, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Udende a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan bayan ya samu kuri’u 135,573, inda ya doke Sanata Suswam wanda ya samu kuri’u 112,231.

Bayan rashin gamsuwa da sakamakon zaben ba, Suswam ya garzaya kotu.

A hukuncin da kotun ta yanke, ta ce Suswam ya samu nasarar kafa hujjar cewa an tafka kura-kurai a kananan hukumomi biyar cikin bakwai na gundumar da aka yi zaben.

Kotun ta soke kuri’u 51,895 da Sanata Udende ya samu, sannan ta soke kuri’u 21,229 da aka kada wa Sanata Suswam.

Bayan rage kuri’un da aka kada, Sanata Suswam ya samu kuri’u 90,590 yayin da Sanata Udende ya samu kuri’u 82,699.

Da yake tabbatar da karar, mai shari’a Ori Zik-Ikeoha ya jagoranci kwamitin yanke hukunci a kan Suswam, inda suka yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yi a baya.

Bama-baman Lakurawa ne suka kashe mutane a Sakkwato – Sojoji

Gobara ta ƙone shaguna da kayan miliyoyi a kasuwar Nasarawa

Abubuwan farin ciki da suka faru a 2024

Gyaran TCN ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a Abuja