Kotu ta kori karar Emefiele da DSS ta shigar

Hukumar DSS za ta sake gurfanar da Godwin Emefiele a ranar 23 ga watan Agustan da muke ciki

Kotu ta kori karar Emefiele da DSS ta shigar

Emefiele a lokacin zaman kotun ranar Alhamis 17 ga Agusta, 2023 a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta yi watsi da ƙarar da hukumar DSS ta shigar kan Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele da aka dakatar.

Mai Shari’a Nicholas Oweibo ya kori karar ce bisa hujjar cewa masu karar ba su bi ka’ida ba, kuma sun raina kotu.

Hakan na zuwa ne a yayin da kotun ta ci gaba da sauraron shari’ar Emefiele, wanda hukumar ta gurfanar kan zargin mallakar haramtattun makamai, wanda daga baya ta nemi janyewa.

A baya kotun ta ba da belin Emefiele a kan Naira miliyan 20, ta ba da umarnin tsare shi a gidan yari har sai ya cika sharuddan da ta gindaya masa.

Sai dai kafin tafiya da shi jami’an DSS suka kwace shi a harabar kotu daga hannun jami’an gidan yari, suka yi awon gaba da shi, da cewa za ta kara zurfafa bincikensa kan wasu batutuwa.

Daga baya hukumar ta janye zargin, ta maka shi a gaba Kotun Birnin Tarayya kan wasu sabbin zarge-zarge 20.

A safiyar Alhamis an kwashi ’yan kallo a kotun na Abuja inda lauyoyinsa suka nemi hana ’yan jarida ɗaukar hotonsa a kotu.

Shigo da shi kotu ke da wuya lauyoyin nasa suka yi tatattare manema labarai da ke son daukar sa hoto; har daga karshe lauyoyin suka kashe fitila.

An ga Emefiele yana yin waya a cikin kotun a safiyar Alhamis, inda lauyoyinsa suka yi ta tattare shi domin hana ’yan jarida ɗaukar sa hoto.

Bayan kai shi kotun ne kuma alkali ya bukaci dage zaman inda ya bukaci hukumar ta sake gurfanar da Emefiele a ranar 23 ga watan Agustan da muke ciki.

Kotu ta dage sauraron ƙarar DSS ne saboda rashin kawo ɗaya wanda ake zargin su tare da Emefiele a zaman kotun na safiyar Alhamis.

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai