Kotu ta kori karar LP kan samun kaso 25 a Abuja kafin a lashe zabe

Hakan ya sanya alkalin kotun fatali da karar da jam’iyyar LP ta shigar.

Kotu ta kori karar LP kan samun kaso 25 a Abuja kafin a lashe zabe

Peter Obi

Kotun sauraren kararrakin zaben Shugaban Kasa ta yi watsi da ikirarin jam’iyyar LP da dan takararta, Peter Obi na cewa dole dan takara ya samu kaso 25 cikin 100 na kuri’un Abuja kafin ya lashe zabe.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Haruna Tsammani ne ya yanke hukuncin yayin zaman kotun na ranar Laraba a Abuja.

A lokacin zaben shugaban kasa na 2023 da aka yi a ranar 25 ga Fabrairu, LP da Obi sun samu sama da kaso 25 ta hanyar samun kusan kaso 59 cikin 100 na kuri’un da aka kada a Abuja.

Shugaban kasa Bola Tinubu na jam’iyyar APC ya samu kashi 19 da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP wanda ya samu kashi 15.

Wannan dalili ne ya sanya LP da dan takararta ikirarin cewar Tinubu bai zama halastaccen shugaban Najeriya ba.

Da ta ke yanke hukunci kan karar, kotun mai mutane biyar ta yi watsi da tuhumar, inda bayyana cewa Abuja kamar sauran jihohi 36 na tarayyar Najeriya ne ba ta da wani fifiko.

A cewar kotun, mazauna birnin tarayya ba su da wata dama ta musamman kamar yadda masu shigar da karar suka yi ikirari.

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara