Kotu ta kori karar neman hana Jonathan takara
Mai Sharia Peter Lifu ya yanke wannan hukunci, bayan ya yi watsi da karar da aka shiga na neman umarnin kotu ta hana Jonathan sake tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a babban zaben da ke tafe.
Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Goodluck Jonathan
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta sahale wa tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Ebele Jonathan, tsayawa takara a zaben 2027.
A safiyar Talatar nan ce Mai Sharia Peter Lifu ya yanke wannan hukunci, bayan ya yi watsi da karar da aka shiga na neman umarnin kotu ta hana Jonathan sake tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a babban zaben da ke tafe.
Mai shigar da kara, Johnmary Jideobi, ya bukaci kotun ta bayar da umarnin hana Jonathan neman takara a zaben 2027 da sauran zabuka.
Karin bayani na tafe…