Kotu ta kori shari’ar da Ochendo ya kai Ibinabo

Wata Babbar Kotu a Legas ta kori karar da dan fim McSmith Ochendo ya shigar, inda yake bukatar kotun ta sauke Ibinabo Fiberesima daga mukaminta na shugabar kungiyar ’Yan Fim Ta Najeriya (AGN).Mai Shari’a J. Yinusa, a Litinin da ta gabata ya yanke hukuncin cewa, karar da Ochendo ya shigar ba ta da sahihanci. A […]

Kotu ta kori shari’ar da Ochendo ya kai Ibinabo

Daga hagu, Ibinabo Fiberisima ce, a dama kuwa Ochendo McSmithWata Babbar Kotu a Legas ta kori karar da dan fim McSmith Ochendo ya shigar, inda yake bukatar kotun ta sauke Ibinabo Fiberesima daga mukaminta na shugabar kungiyar ’Yan Fim Ta Najeriya (AGN).
Mai Shari’a J. Yinusa, a Litinin da ta gabata ya yanke hukuncin cewa, karar da Ochendo ya shigar ba ta da sahihanci. A karar da dan wasan ya shigar, ya nemi a cire Ibinabo daga mukaminta saboda a cewarsa, an taba kama ta da laifi har ma aka daure ta.
Mai Shari’ar ya bayyana cewa Ochendo ba ya da ikon da zai nemi a cire Ibinabo daga mukaminta, domin kuwa ba ya cikin ’yan takarar da suka nemi mukamin nata. Saboda haka ne ma ya kori shari’ar saboda ba ta da sahihanci.
A nasa bangaren, a lokacin da yake magana da ’yan jarida, Ochendo ya ce zai daukaka kara. A cewarsa, babban dalilin da ya sa ya shigar da karar, ba a bincike shi ba ma sam, balle ma mai shari’ar ya hankalta da shi. Ya ce, tun da farko, Ibinabo bai kamata a ce ta tsaya takarar shugabancin kungiyar ’Yan Fim Ta Najeriya ba.
Ita kuwa Ibinabo, farin ciki ta nuna da sakamakon shari’ar, inda ta nuna cewa nasarar ba tata ba ce ita kadai, nasara ce ga ’ya’yan kngiyar gaba daya.
Ibinabo dai ta yi shekara daya ke nan kan wannan mukami, domin kuwa an rantsar da ita ne a watan Nuwamba na bara. Wasu daga ’yan wasa sun bayyana cewa ta yi wa kungiyar tasu kokari tun fara mulkinka, domin kuwa ta samar masu da doguwar bas mai daukar mutum 18, sannan kuma tana kokarin kawo shirin bunkasa lafiya ga ’yan wasa.