Kotu ta kwace gidaje 753 a hannun jami’in gwamnati daya
Kotu ta kwace kwace gidaje 753 daga wani tsohon jami’in gwamnati wanda EFCC ta kama kan zargin sace kudaden al’umma a Abuja.
Kotu ta kwace kwace rukunin gidaje 753 daga wani tsohon jami’in gwamnati da ake zargi da ruf-da-ciki a kan kudaden al’umma a Abuja.
Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie ya ba da umarnin kwace gidajen ne a ranar Litinin a ci gaba da shari’ar da Hukumar yaki da Masu Karya tattalin Arzikin Kasa (EFCC) ta gurfanar da wanda ake zargin.
Kwace gidajen da ke Cadastral Zone C09, Lokogoma, Abuja, shi ne kwacen kadarori mafi girma a lokaci guda da hukumar EFCC ta yi nasara yi tun da aka kafa ta shekara 21 da suka gabata.
Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Onwuegbuzie, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya kasa kawo gamsasshend dalilin da zai hana kwace kadarorin, “wadanda ake zargin ya mallake su ta haramtacciyar hanya, don haka an mallaka wa gwamnati tarayya gidajen.”

Kafin wannan hukunci, a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2024, kotun ta ba da umarnin wucin-gadi na mallaka wa gwamnati gidajen da EFCC ke gudanar da bincike a kansu.
Sanarwar da EFCC ta fitar na nuni da cewa, shugabanta, Ola Olukoyede, ya bayyana hukuncin a matsayin mahangurba ga masu sace dukiyar kasa.