Kotu ta kwace gidajen N11bn a hannun Emefiele

Ana zargin Emefiele ya yi amfani da wasu mutane wajen sayen gidajen alfarma da kudaden haram a Abuja

Kotu ta kwace gidajen N11bn a hannun Emefiele

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta kwace karin gidajen da darajarsu ta kai Naira biliyan 11 daga tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Mai Sharia’a Chukwujekwu Aneke ya ba da umarnin wucin gadin mallaka wa Gwamnatin Tarayya gidajen nen, bayan sauraron bayanin lauyoyin hukumar yaki da masu karya tattalin arzikin kasa (EFCC),  karkashin jagorancin Rotimi Oyedepo (SAN).

EFCC ta gurfanar da Emefiele a Legas ne bisa zargin amfani da ofishinsa wajen azurta kansa da wasu almundahana.

Rotimi Oyedepo ya shaida wa kotun cewa ana zargin Emefiele ya yi amfani da wasu mutane wajen sayen gidajen alfarma da kudaden haram a unguwannin masu fada a ji, musamma a Abuja.

EFCC ta bayyana wasu jami’an CBN uku, Obayemi Oluwaseun Teben, Akomolafe Adebayo da kuma Olubunmi Makinde a matsayin wadanda suka taimaka wa Emefiele da matsayinsu wajen yin ciniki da kuma bayar da kaso na musamman na kudaden kasashen waje ga wasu kamfanonin canji domin karbar nagoro.

Alkali ya umarci hukumar EFCC ta wallafa bayanan gidaden da za a kwace a jarida domin duk wanda ke da magana ko kalubalantar hakan ya yi kafin a mallaka wa gwamnati gidajen gaba daya.

Daga nan ya dage zaman zuwa ranar 21 ga wannan watan da muke ciki domin ba da umarnin karshe na  mallaka wa gwamnati gidajen da aka kwace.