Kotu ta tabbatar da Sanusi II a matsayin Sarkin Kano
Kotu ta tabbatar da nadin Sarki Muhammadu Sanusi II, ta kuma haramta wa wadanda aka tube bayyana kansu a matsayin sarakuna
Babbar Kotun Kano ta umarci sarakunan masarautun jihar da aka tube da su mayar mata da duk wani kaya mallakar gwamnati da ke hannunsu.
Kotun ta tabbatar da nadin Sarki Muhammadu Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16, ta kuma haramta wa wadanda aka rusa masarautun nasu bayyana kansu a matsayin sarakuna.
Da take yanke hukuncin a ranar Alhamis, Mai sharia Amina Adamu Aliyu ta tabbatar da ikon da Majalisar Dokokin Jihar Kano na yin dokokok.
Alkalin ta ci gaba da cewa don haka gyaran dokar masaraun jihar da majalisar ta yi yana kan daidai, haka ma hannun da Gwamna Abba Kabir ya yi a kan dokar wadda ta nada Sarki Muhammadu Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16, bai saboda doka ba.
- Hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.19
- Yadda aka kasa gyara titin Kaduna-Abuja a shekaru 6
Sai dai kotun ta ki amincewa da rokon masu kara na cewa a fitar da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero daga Fadar Nassarawa.
Alkalin ta ce wannan ba hurumin kotun ba ne sai dai su kai wannan bukatar ga kotun tirabunal.