Kotu ta kwace kujerar Sanata da dan majalisar PDP a Filato

Kotu ta soke nasarar Sanata Napoleon Bali da Honorabul Peter Gyendeng na PDP a zaben 2023

Kotu ta kwace kujerar Sanata da dan majalisar PDP a Filato

Kotun sauraron kararrakin zabe ta kwace kujerar Sanatan Filato ta Kudu, Napoleon Bali na jam’iyyar PDP.

Kotun ta kuma soke zaben Peter Gyendeng, dan majalisar wakilai mai wakiltar Barikin Ladi/Riyom, a karkashin inuwar jam’iyyar.

Kotun ta sanar da tsohon Gwamnan Jihar Filato kuma Minista Kwadago, Simon Bako Lalong na Jam’iyyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan, sai kuma Fom Dalyop na Jam’iyyar LP a matsayin zababben dan majalisar wakilai na mazabar Barikin Ladi/Riyom.

’Yan takarar APC da LP sun garzaya kotun ne domin neman ta soke zaben Napoleon Bali da Peter Gyendeng na PDP ne, a bisa hujjar cewa jam’iyyar suka yi wa takara ba ta da shugabanci, don haka ba ta da hurumin tsayar da dan takara.

A bisa haka ne Mai Shari’a Omaka Elekwo da kuma Muhammad Tukur suka soke zabukan mambobin PDP, saboda saba dokar zabe da bijirewar jam’iyyar ga umarnin Babbar Kotun da ke Jos na gudanar da zaben shugabanni kafin babban zaben da ya gabata.

Alkalan sun bayyana cewa hujjojin da APC da LP suka gabatar sun gamsar da su, don haka sun soke duk kuri’un da aka kada wa ’yan takarar PDP a zaben.

Yadda sojoji suka kashe ’yan ta’adda 481 suka kama 741 a wata guda

Yau za a yi jana’izar Janar Lagbaja

NAJERIYA A YAU: Shirin Da Masu Ruwa Da Tsaki Suka Yi Kan Zaben Ondo.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu