Kotu ta kwace lasisin bindigar wanda karensa ya harbe shi
Wata kotun kasar Jamus ta kwace lasisin wani dan kasar bayan da karensa ya harbe shi, kamar yadda jaridar The Independent ta sanar. A ranar Tatatar makon jiya ne kotun da ke birnin Munich ta Jihar Babaria da ke Jamus ta yi watsi da daukaka karar da wani mutum ya shigar don a dawo masa […]
Wata kotun kasar Jamus ta kwace lasisin wani dan kasar bayan da karensa ya harbe shi, kamar yadda jaridar The Independent ta sanar.
A ranar Tatatar makon jiya ne kotun da ke birnin Munich ta Jihar Babaria da ke Jamus ta yi watsi da daukaka karar da wani mutum ya shigar don a dawo masa da lasisin mallakar bindiga da hukumomin Babaria suka kwace.
Wannan hukuncin ya biyo bayan tsautsayi da ya faru a shekarar 2016 tsakanin wani mutum da aka sakaya sunansa da karensa da ba a bayyana jinsinsa ba.
Yadda karen ya harbi mutumin da ya mallake shi
Rahoton bai yi cikakken yadda harsashin bindigar ya shiga jikin mutumin ba. Sai dai ya bayyana cewa karen ya latsa kunamar bindigar da ke da harsasai a ciki ne lokacin da aka ajiye bindigar a cikin motar suna tare da mutumin. Bayan latsawar da karen ya yi sai ta harbi mutumin a hannunsa kusa da kafadarsa.
A cewar kotun mutumin da yake sha’awar farauta ba za a iya yarda da shi ba wajen sarrafa bindiga yadda ya dace ba, saboda hakan ya nuna cewa nan gaba, idan ya mallaki bindiga zai iya yi mata rikon sakaci ba tare da lura ba, kamar yadda majiyar The Independent ta ce.
Sai dai mutumin zai iya daukaka kara zuwa kotun gaba.
Ko irin wannan abin ya taba faruwa?
A watan Nuwamba, wani dan Jihar New Meziko da ke Amurka mai suna Sonny Gilligan ya shirya tsaf don tafiya wajen farauta sai karen da suke tare a cikin wata mota kirar Fijo ya harba bindigar Sonny. Kafin karen ya harba bindigar sai da ya boye kansa a jikin kujerar direban mota, amma duk da haka daga bisani sai da karen ya yi harbin, kamar yadda kafar sadarwa ta WTOP-FM ta sanar.
Sonny sai da ya nemi agaji daga wanda yake kusa. Ya ce, “Wane ne a nan ?” Ina wurin ni kadai babu kowa. Kamar yadda ya bayyana wa majiyar WTOP-FM
Bayan ya fita daga cikin motar karen nasa mai suna Charlie, ya samu nasarar latsa kunamar bindigar kuma ya yi harbi da bindigar.
A lokacin da Sonny ya fita daga cikin motar ya kira lambar neman agaji ta 911. Sannan aka kai shi asibitin garin, inda likitoci suka samu rauni a huhunsa da karyewar kasusuwa uku na kirjinsa da karaya a kashin da ya rike kafadunsa.
Sonny ya ce, wannan labari ne da kowa zai yi sha’awa a ce kare ya harbi mutum, kamar yadda ya bayyana wa majiyar WTOP-FM
Sonny mai shekara 74 ya ce, ya yafe wa karensa a kan laifin harbin da ya yi masa.
Sonny ya kara da cewa, “karena mai suna Charlie bai harbe ni da gangan ba, Karen yana da kyau”, inji shi.