Kotu ta kwace kujerar Sanata Elisha Abbo

Kotun ta ayyana Amos Yohanna na jam’iyyar PDP a matsayin Sanatan Adamawa ta Arewa.

Kotu ta kwace kujerar Sanata Elisha Abbo

Sanata Elisha Abbo

Kotun Daukaka Kara ta soke nasarar dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Sanata Elisha Ishaku Abbo na jam’iyyar APC.

Kotun ta ce abokin takararsa, Amos Yohanna na jam’iyyar PDP ne halastaccen wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Fabrairu.

Kotun mai alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari’a C.E. Nwosu Iheme, ta kuma umarci Hukumar Zabe ta Kasa INEC da ta karbe shaidar lashe zabe da ta bai wa Sanata Abba.

Aminiya ta ruwaito cewa, INEC ce ta ayyana Mista Abbo a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Adamawa ta Arewa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Hakan ce ta sanya Mista Yohana na jam’iyyar PDP ya kalubalanci sakamakon a Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da ke zaman a Yola, babban birnin Jihar Adamawa.

Sai dai kotun sauraron kararrakin zaben ta yi fatali da korafin da Mista Yohanna ya gabatar tana mai cewa ba shi da gamsassun hujjoji.

Bayan sauraron korafin Mista Yohanna a Kotun Daukaka Kara, kai tsaye hujjarsa ta samu gindin zama bisa la’akari da sashe na 137 da ke Kundin Dokar Zabe ta 2022.

NAN

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan

A tabbatar an mutunta tsarin dimokuraɗiyya a Zaɓen Edo — Tinubu