Kotu ta nemi ’yan sanda su biya kungiyar MOSSOB diyya
Babbar Kotun Jihar Ebonyi a zamanta na Abakalike, ta umarci rundunar ’yan sandan jihar ta biya kungiyar fafutukar kafa yankin Biyafara (MASSOB) diyyar Naira miliyan biyu sakamakon kai samame a ofishinta ba bisa ka’ida ba.Aminiya ta samu bayanin wani daga cikin jagororin kungiyar mai suna John Nwifuru ne ya gurfanar da kwamishinan ’yan sandan jihar […]
Babbar Kotun Jihar Ebonyi a zamanta na Abakalike, ta umarci rundunar ’yan sandan jihar ta biya kungiyar fafutukar kafa yankin Biyafara (MASSOB) diyyar Naira miliyan biyu sakamakon kai samame a ofishinta ba bisa ka’ida ba.
Aminiya ta samu bayanin wani daga cikin jagororin kungiyar mai suna John Nwifuru ne ya gurfanar da kwamishinan ’yan sandan jihar da kuma jami’in shiyya (DPO) da mai kula babban ofishin rundunar da kuma mai kula da sashenaikata manyan laifuka (DCO) gaban kuliya a bara, yana zargin kai samame a ofishin shiyya na kungiyar da ke Abakalike, suka tafi da wasu kayayyaki.
A hukuncin da ya yake, Mai shari’a F.C. Inya-Agha ya ce, “Abin da ’yan sandan suka yi ya saba doka ta 34 da 35[1] sashe na 40 da 44 na tsarin mulki da ya haramta cin mutunci ko kama mutane ba bisa ka’ida ba da kuma kwasar dukiya”. Sai ya nemi, ba tare da wani jinkiri ba, ’yan sandan su mayar da kayan da suka kwashe.
Daga cikin kayan akwai katin shaida na ’yan kungiyar guda 2,700 da kujeru goma wayar salula biyar da tutocin kungiyar da kuma Naira dubu 170.
Haka nan alkalin ya nemi DPO ya rubuta takardar neman afuwa ga kungiyar cikin jaridu biyu na kasar nan.
Lauyan kungiyar, Mista Jerry Ezenyi ya bayyana farin cikinsa da hukuncin da kotun ta yanke.