Kotu ta raba auren shekara 21 saboda ‘babu soyayya’ a tsakanin ma’auratan

Matar ta ce mijin ya daina son ta

Kotu ta raba auren shekara 21 saboda ‘babu soyayya’ a tsakanin ma’auratan

Ma’aurata

Wata kotun yanki da ke Igboro a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, ta raba wani auren shekara 21 tsakanin mata da miji saboda da ta ce mijin ya daina son ta.

Matar, mai suna Isiwatu Ibrahim, dai ta shigar da mijin nata mai suna Mumini Kadri kara ne tana neman a ba ta ikon kula da ’ya’yansu bayan an raba auren saboda ya daina son ta.

Alkalin kotun, Mai Shari’a AbdulQadir Umar, ne ya sanar da rushe auren saboda ma’auratan sun ki su sasanta tsakaninsu.

Daga nan ne alkalin ya ba ta damar ci gaba da kula da yaran nasu guda hudu, amma ya bukace ta da ta kammala Iddah kafin ta sake yin wani sabon auren, kamar yadda Shari’ar Musulunci ta tanada.

Matar ta kuma shaida wa kotun cewa a shirye take ta ci gaba da daukar nayin yaran ko da tallafin tsohon mijin nata, ko babu.

To sai dai wanda ake karar ya roki kotun da ta taimake shi kada ta raba auren nasu.

Ya ce shi dan acaba ne da yake tuka babur mai kafa uku, kuma ba shi da lokacin kula da ’ya’yan nasu.

(NAN)

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja