…Kotu ta raba gardamar da ta sarke a tsakanin wadansu kurame biyu
Kimanin watanni biyu ke nan aka kwashe ana shari’a a tsakanin wadansu kurame biyu masu suna Oti Adjei da Richard Tsibu a kotun majistare da ke a Swedru da ke Ghana. Su dai kuramen kowanensu yana ikikarin jaririn nasa ne bayan sun nemi uwar jaririn mai suna Freda Ansah da ita ma kurma ce a […]
Kimanin watanni biyu ke nan aka kwashe ana shari’a a tsakanin wadansu kurame biyu masu suna Oti Adjei da Richard Tsibu a kotun majistare da ke a Swedru da ke Ghana. Su dai kuramen kowanensu yana ikikarin jaririn nasa ne bayan sun nemi uwar jaririn mai suna Freda Ansah da ita ma kurma ce a lokuta daban-daban. Sai dai gwajin jinin kuramen da kotun ta sa aka gudanar a wani asibiti mai suna Trust Hospital ya nuna daya daga cikin kuramen mai suna Oti Adjei ne ya mallaki yaron.
Tun a watan Janairu wannan shekara da muke ciki ne dai gardama ta sarke a tsakanin Tsibu wanda mai sana’ar gyara takalma ne da kuma Adjei wanda bai aikin komai kuma dukansu kurame ne sun nuna sun kwanta da uwar yaron mai suna Freda Ansah wacce ita kanta bebiya ce.
Kotun a bisa shugabancin Mista Issac Apeatu, da ta umurci yin gwajin jini a tsakaninsu da aka fi sani da DNA ta ce , yanzu dai ta tabbata da na Adjei ne, kuma yana da damar ya rada masa suna a yanzu tun da an fara shari’ar ce tun jaririn yana da watanni biyu.