Kotu ta rufe aususun Gwamnatin Kano a CBN da sauran bankuna —Lauyan ’yan kasuwa
Ayagi ya ce umarnin kotu zai hana gwamnatin taba kudadenta da take da su a yanzu da ma wadanda nan gaba za su shiga asusun ajiyarta da ke CBN da sauran bankuna.
Lauyan ’yan kasuwar Kano masu shaguna a Filin Idi na Kofar Mata, Nuruddeen Ayagi, ya ce umarnin biyan diyyar Naira biliyan 30 da kotu ta ba wa gwamnatin jihar yana nufin rufe asusun gwamantin da ke bankuna.
Ayagi ya ce saboda haka, gwamnatin ba za ta iya amfani da kudaden da take da su ko wadanda a nan gaba za su shiga asusun ajiyarta da ke Babban Bankin Najeriya (CBN) da sauran bankuna 20 ba.
Aminiya ta ruwaito cewa Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta umarci gwamnatin jihar da ’yan kasuwar Filin Idi na Kofar Mata Naira biliyan 30 a matsayin diyyar da rusau da ta yi musu.
Mai Shari’a I.E Ekwo ya ba da umarnin da ke tilasta gwamantin da biya diyya ne bayan da farko Mai Shari’a Simon Ademola ya ba da umarnin hakan bayan sauraron wadanda aka rushe wa shaguna a Filin Idi.
- Hukumar Shari’a ta dakatar da alkali kan yanke hukunci ta hanyar da ba ta dace ba
- Tudun Biri: An fara tattauna biyan diyyar Harin Mauludi
Mai Shari’a Ekwo ya kuma bukaci gwamnatin jihar ta bayyana a gabanta ranar 18 ga Janairu, 2024, ta kare kanta, ko akwai dalilin da zai hana biyan kudin daga asusun bankinta.
Ayagi ya ce umarnin kotun ya far aiki, “daga ranar da aka bayar da umarnin kotun ga CBN da ma duk bankin ko cibiyoyin kudi da ya shafa, za su rufe asusun Gwamnatin Kano da ke hannunsu.
“Kotun ta kuma ba wa gwamnatin ranar 18 ga Janairu ta zo ta kawo dalilin da zai hana a umarci bankunan su amfani kudin gwamnatin da ke hannun su su biya ’yan kasuwar Filin Idi na Kofar Mata diyyar barnar da gwamnatin ta yi musu a rusau da ta yi ranar 4 da 5 ga watan Yuni, 2023 ba.
A kan haka ne wakilinmu ya nemi ji daga Akanta-Janar na jiahr, Abdulkadir Abdulsalam, domin yadda gwamnatin za ta gudanar da harkokinta da kuma biyan albashin ma’aikata, a wannan yanayi.
Sai dai jami’in ya bukaci wakilinnamu ya tuntubi ofishin Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a na jihar, Haruna Isa Dederi