Kotu ta sa a yi wa Murja gwajin kwakwalwa
Kotun Muslunci ta sa a yi wa jarumar TikTok Murja Kunya gwajin kwakwalwa
Kotun Muslunci da ke zama a unguwar Gama a Kano ta sa a yi wa jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya gwajin kwakwalwa.
Mai Shari’a Nura Yusuf ya ba da umanrin yi wa Murja gwajin kwakwalwa a asibitin gwamnati domin tabbatar da lafiyar kwakwalwarta.
Alkalin ya ba da umarnin ne bisa zargin ba ta cikin hayyacinta a lokacin zaman kotun na farko da aka gurfanar da ’yar TikTok din.
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce ta gurfanar da Murja kan zargin tayar da hankalin jama’a, bata tarbiyya da kuma koyar da karuwanci.
- Hisbah ta cafke ’yan kasar waje kan aikata badala a Kano
- Murja da Hisbah: Yau za a ci gaba da shari’a
A zaman na ranar Talata alkali ya ba da umarnin a ci gaba da tsare Murja a ofishin hukumar Hisbah, wadda ita kuma za ta rika ba wa kotu bayani kan halin da ’yar TikTok din ke ciki.
Daga nan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Mayu.
Aminiya ta gabo cewa jami’an hukumar tsaro ta DSS ne suka kai Murja kotun a zaman na ranar Talata.
Da farko, alkali ya sa a tsare Murja a gidan yarin Kurmawa ne bayan ta musanta zarge-zargen da hukumar Hisbah ta gurfanar da ita a kansu.
An sake gurfanar da Murja a karo na biyu ne bayan kurar da ta tashi a Kano kan sakin ta daga gidan yarin da ake tsare da ita, sabanin umarnin alkali a lokacin zaman farko.
Jami’an Hisba suka tsare Murja ne sakamakon korafe-korafen da hukumar ta samu a kanta daga mazauna unguwar tinshama, inda take da zama.
Jama’ar unguwar sun koka da cewa Murja tana kawo musu bata-gari da tsakar dare, gami da yi musu barazana ta kafofin sada zumunta, lamarin da ke razana su.
Da yake jawabi kan sakin Murja daga gidan yari da kuma fifikon da aka ba ta, Kwamishinan yada Labaran Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya ce akwa sabbin zarge-zarge da take fuskanta shi ya sa jami’an tsaro suka dauke ta daga gidan yari domin ta je ta amsa tambayoyi.