Kotu ta sa Murja Kunya da abokanta sharar asibiti da masallaci

Murja za ta yi sharar asibiti, aboknata kuma, za su rika sharar masallaci

Kotu ta sa Murja Kunya da abokanta sharar asibiti da masallaci

Kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Filin Hokey ta yanke jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya da abokanta hukuncin sharar masallaci da kuma asibiti.

Abokan Murja maza, wadanda aka gurfanar da su tare da ita, Ashiru Idris Mai Wushirya, Aminu BBC da kuma Sadiq Shehu Shariff, za su zai rika sharar Masallaci Murtala da ke Kano, da bandakunansa na tsawon mako uku.

Ita kuma za ta rika share Asibitin Murtala, ta rika zuwa tana yin awa 8 kullum a ofishin Hisbah, ta goge  wasu bidiyonta a shafukan sada zumunta, sannan an haramta mata gudanar da taron jama’a.

Kotun ta yanke musu hukuncin ne a shari’ar da aka gurfanar da su kan zargin yada batsa a kafar TikTok da kuma bata tarbiyya, zargin da suka musanta.

Gabanin zaman kotun na ranar Alhamis, sai da alkali, Mai shari’a Abdullahi Halliru, ya tura su zaman wakafi a gidan yari a kan zargin.

A zaman na ranar Alhamis, mai gabatar da kara, lauyan Gwamnatin Jihar Kano, Barista Lamido Abba Soron Dinki, ya roki kotun da a sake karantawa Murja takardar tuhumar da ake mata na yin batsa, tayar da hankali da barazana ga zaman lafiya a cikin al’umma, wanda hakan ya saba wa sashi na 355 da na 33 da na 275 na Kundin Shari’ar Musulunci.

Sannan ya gabatarwa kotun takardar yarjejeniyar sulhu da Murja ta rubuta kan cewa ta amsa laifinta ta hannun lauyanta Barista A E Saka.

Daga nan ne Mai Shari’a Abdullahi Halliru ya yi umarnin da a karanta mata takardar hukuncinsa.

Takardar ta kunshi cewa dole ne ita wacce ake tuhuma Murja Ibrahim Kunya ta goge dukkanin wani bidiyo ko sauti da ta wallafa mai dauke da batsa daga shafukanta na sada zumunta.

An hana haramta wa Murja shirya duk wani nau’in taro na jama’a da zai iya jawo batanci ko bata tarbiyya ko tayar da tarzoma ko tayar da hankalin al’umma.

Sai kuma sharadin zuwa ofishin Hukumar Hisba a duk ranakun Litinin da Alhamis daga karfe 12 na rana zuwa 5 na yamma har na tsawon wata shida.

Haka kuma za ta rika gabatar da kanta a kotu duk bayan wata daya tare da ma’aikacin Hukumar Hisba.

Takardar Kotun ta ce saba wa wadannan sharuda zai iya janyowa a kara mata lokaci a kan wanda kotun ta sanya mata na watanni shida.

Bayan karanta mata ne Mai Shari’a ya tambayi Murjar ko ta gamsu, nan take ta amsa cewa ta yarda.

Idan za a iya tunawa, Majalisar Malamai ta Jihar Kano ita ce ta yi karar Murja Ibrahim Kunya ga ’yan sanda inda su kuma suka gurfanar da ita a gaban kotu.

Ana tuhumar Murja da laifin hada kai da Sanusi Oscar 442 da Safara’u da Dan Maraya, da Amude Booth da Samha M. Inuwa da Ummi Shakira, wadanda a yanzu haka suka cika wandonsu da iska, inda suke bin wata waka ta Ado Gwanja da Kawo Dan Sarki inda suke yada shi a shafukan sada zumunta wanda hakan zai iya bata tarbiyan al’ummar Jihar Kano.