Kotu ta sakaya mai yunkurin lalata yarinya a kurkuku

A ranar Litinin da ta gabata ne aka gurfanar da wani matashi dan shekara 32 mai suna Abubakar Musa da ke zaune a unguwar Idi a gaban kotun yanki ta Doma a garin Gombe. dan sanda mai gabatar da kara, Sajen Aliyu Muhammad, ya shaida wa kotu cewa a ranar 18 ga wannan watan ne, […]

Kotu ta sakaya mai yunkurin lalata yarinya a kurkuku

A ranar Litinin da ta gabata ne aka gurfanar da wani matashi dan shekara 32 mai suna Abubakar Musa da ke zaune a unguwar Idi a gaban kotun yanki ta Doma a garin Gombe.

dan sanda mai gabatar da kara, Sajen Aliyu Muhammad, ya shaida wa kotu cewa a ranar 18 ga wannan watan ne, da misalin karfe daya na rana suka kama Abubakar Musa a makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Unguwar Malam Inna yana kokarin aikata laifi. Sajen ya ce wasu mutane suka kama shi yana cire al’aurarsa, yana bai wa wata yarinya da aka sakaye sunanta, ’yar shekara 13 tana masa wasa da shi. Ya ce aikata hakan laifi ne da ya saba wa dokar kasa, sashi na 95 na kundin laifuffuka da hukunci na Finalkod.

Da kotu ta tambayi wanda ake zargi, bai musanta zargin ba, ya amince da laifinsa. Don haka sai Alkalin kotun mai shari’a Barista Aminu Haruna ya yi amfani da wannan sashi na 95 ya tura shi gidan kurkuku zuwa ranar Litinin domin ci gaba da sauraron shari’ar.