Kotu ta sake bayar da belin Emefiele kan miliyan 300
An gurfanar da Emefiele ne kan zargin yin almundahana da kuma wasu laifuka.
Wata Babbar Kotu a Abuja ta bayar da bayar da belin tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele kan kudi Naira miliyan 300.
Mai Shari’a Hamza Mu’azu ya kuma umarci Emefiele da ya gabatar da mutum biyu wadanda za su tsaya masa don cika sharuddan belin.
- Kano: Kundin shari’ar Kotun Daukaka Kara ya tabbatar da nasarar Abba —Dederi
- Abba ya sake gabatar da ƙwarya-ƙwaryan kasafin kudin Kano
Mu’azu ya ba da umarnin cewa wadanda za su tsaya masa dole ne su mallaki takardar shaidar zama da kuma su kasance suna da kadarori a gundumar Maitama da ke Abuja.
Kazalika, dole Emefiele ya damka wa magatakardar kotun fasfo dinsa, kuma dole ne ya ci gaba da zama a Abuja.
Emefiele zai ci gaba da zama a gidan gyaran hali na Kuje har sai ya cika sharudan belin da kotun ta gindaya masa.
Wannan na zuwa ne bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta bayar da belin Emefielen a kan kudi Naira miliyan 20.