Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da sabon umarnin dakatar da Babban Taron Jam’iyyar PDP da ake shirin gudanarwa ranar 15 da 16 an watan nan a Ibadan, fadar Jihar Oyo

Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sake hana Babban Taron Jam’iyyar PDP da ake shirin gudanarwa ranar 15 da 16 an watan nan a Ibadan, fadar Jihar Oyo.

Umarni na uku masu karo da juna ke nan da kotu ta bayar kan taron babbar jam’iyyar adawar mai cike da ruɗani.

Kotun ta kuma haramta wa Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) sa ido, sa hannu ko amincewa da duk wani sakamako da zai fito daga taron, inda ake sa ran za a zaɓi shugabannin jam’iyyar na ƙasa.

Mai Shari’a Peter Lifu ne ya bayar da umarnin hana gudanar da taron a ranar Talata, yayin da yake yanke hukunci kan ƙarar da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido ya shigar.

Lamido ya kai ƙarar jam’iyyar ne bisa zargin cewa an hana shi da gangan sayen fam ɗin takarar shugabancin jam’iyyar na ƙasa, lamarin da ya ce ya tauye masa haƙƙinsa na shiga cikin zaɓen.

Mai Shari’a Lifu ya bayyana cewa dole ne kotu ta bayar da wannan umarni, saboda PDP ta gaza bin dokokin da suka shafi gudanar da irin wannan taro.

Ya ce shaidun da ke gaban kotu sun nuna cewa jam’iyyar bata fitar da jadawalin taron ba kamar yadda doka ta tanada, wanda hakan ya nuna an karya tsarin da ya dace a bi.

Alƙalin ya ƙara da cewa lamarin ya fi sauƙi ga Lamido, domin idan aka ci gaba da taron ba tare da an ba shi damar shiga ba, zai fuskanci babban hasara da rashin adalci.