Kotu ta sake fatali da buƙatar belin Abba Kyari

Kotun ta ce hujjojin da Abba Kyari ya gabatar ba su da madogara ballantana makama ta fuskar shari’a.

Kotu ta sake fatali da buƙatar belin Abba Kyari

Abba Kyari yayin zaman kotun na ranar Litinin

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da buƙatar neman sabon beli da dakataccen Kwamishinan ’yan sanda, Abba Kyari ya gabatar.

Abba Kyari wanda yake fuskantar tuhumar safarar miyagun ƙwayoyi ya buƙaci a ba da belinsa har zuwa lokacin da za a kammala shari’arsa.

A hukuncin da kotun ta yi wanda mai shari’a Emeka Nwite ya yanke a ranar Laraba, ya ce buƙatar Abba Kyari ba ta da madogara.

Alƙalin kotun ya bayyana cewa dakataccen kwamishinan ’yan sandan bai kawo wani ƙwaƙƙwaran dalilin da zai sanya a ba da belinsa ba.

Mai shari’a Nwite ya nuna cewa kotun ko a baya ta yi watsi da irin wannan buƙatar belin da ya nema tare da ba da umarnin a gaggauta sauraron ƙarar.

Ya bayyana cewa ba a kawo wata hujja wacce za ta sanya kotun ta sauya matsaya kan hukuncin da ta yi a baya ba.

Dangane da hakan ne kotun ta ƙi amincewa da ba da belin sannan ta bai wa hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi NDLEA damar ci gaba da tuhumar Abba Kyari da sauran waɗanda ake ƙara a shari’ar.

Hukuncin na zuwa ne kusan wata ɗaya bayan kotun ta bai wa Abba Kyari beli na wucin gadi domin ya halarci zaman makokin mahaifiyarsa da ta riga mu gidan gaskiya a watan da ya gabata.

A shekarar 2022, hukumar ’yan sandan Nijeriya ta dakatar da Kyari da wasu manyan jami’an ’yan sanda biyu — Sunday Ubua da James Bawa — kan zargin hannunsu a hada-hadar hodar iblis da ta shafi mataimakin kwamishinan ’yan sandan da aka dakatar.

Daga bisani kuma hukumar ta NDLEA ta bayyana neman Abba Kyari ruwa a jallo bisa zargin alaƙarsa da wata ƙungiyar masu safarar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa.

Tun a wancan lokaci, mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babalola, ya bayyana cewa Abba Kyari da tawagarsa sun wawure kilo 15 daga cikin 25 na hodar iblis da suka kwace a hannun wasu baƙi da suka shigo Nijeriya daga Habasha.

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Najeriya

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji