Kotu ta sake soke zaben ’yan majalisar PDP 2 a Filato
Hakan na zuwa ne bayan kotun ta kwace kujerar sanata da ta ɗan majalisa daga PDP a jihar
Kotun sauraron kararrakin zabe a Jihar Filato ta soke zaben kujerun ’yan Majalisar Wakilai 2 ’yan jam’iyyar PDP daga Jihar.
’Yan majalisar da hukuncin ya shafa su ne na Jos ta Kudu da Jos ta Gabas, Musa Bagos, da na Langtang ta Kudu da Langtang ta Arewa, Beni Lar.
- A yi bincike kan yawan kifewar kwale-kwale a Najeriya – Tinubu
- Abin da ya hana matatar man Dangote fara aiki bayan wata 4 da kadadamarwa
Sun dai fafata ne a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu, a karkashin jam’iyyar PDP.
Sai dai kotun ta ayyana Alfred Ajan na jam’iyyar LP da Vincent Mark na APC, wadanda suka zo na biyu a zaben a matsayin halastattun wadanda suka lashe shi.
Kotun dai ta soke zaben ’yan majalisar masu ci ne saboda jam’iyyarsu ta PDP ba ta da shugabanci kuma ba ta gudanar da tarukanta a matakin mazaba ba, kamar yadda babbar kotun tarayya da ke Jos ta yanke hukunci a 2021.
Da suke yanke hukuncinsu daban-daban, Mai Shari’a Omaka Elekwo da Mai Shari’a Muhammad Tukur, sun ce sun soke shi ne saboda jam’iyyar ta ki mutunta hukuncin kotun.
Alkalan sun ce hujjojin da LP da APC suka gabatar kwarara ne kuma karbabbu, don haka dukkan kuri’un da aka kada wa PDP sun zama lalatattu.
Ko a ranar Litinin sai da kotun ta soke zaben Sanatan Filato ta Kudu, Napoleon Bali da dan majalisar mazabar Barikin Ladi/Riyom, Peter Gyendeng, dukkansu na jam’iyyar PDP.
Daga bisani dai ta ayyana tsohon Gwamnan Jihar kuma Ministan Kwadago, Simon Lalong na APC da cewa shi ya lashe zaben Sanatan, sannan Fom Dalyop na LP ne ya lashe zaben dan Majalisar.