Kotu ta sallami amaryar da ta kashe mijinta
Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta sallami Wasila Tasi’u da ake zargi da sanya shinkafar bera a cikin abincin angonta lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa da wasu mutum uku. Waisla mai kimanin shekara 14 da mutumiyar kauyen ’Yansoro ne da ke karamar Hukumar Gaya a Jihar Kano, ta fuskanci tuhumar kisan mijinta ne da […]
Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta sallami Wasila Tasi’u da ake zargi da sanya shinkafar bera a cikin abincin angonta lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa da wasu mutum uku.
Waisla mai kimanin shekara 14 da mutumiyar kauyen ’Yansoro ne da ke karamar Hukumar Gaya a Jihar Kano, ta fuskanci tuhumar kisan mijinta ne da abokansa su uku a watan Maris din bara.
Sallamar wacce ake zargin ya biyo bayan takardar da tsohon Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano Malki Kuliya Umar ya rubuta ne na janye karar. A yayin zaman kotun a ranar Talatar da ta gabata Alkalin Kotun Mohammed Yahaya ya ce “Ba ni da zabi da ya wuce na bayyana cewa dangane da takardar nema tare da sanya hannu da Kwamishinan Shari’a ya yi a kan dakatar da wanann shari’a, kotu ta sallami Wasila Tasi’u.”
A wani labarin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta fara tuhumar wasu jami’anta kan kisan Farfesa Ahmad Mustapha Falaki na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Mataimakin Sufeton Yan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta daya AIG Tambari Yabo Mohammed shi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Kano. Farfesa Falaki wanda shi ne Daraktan Cibiyar Aikin Gona ta Jamai’ar Ahmadu Bello an kashe shi ne a garin Fala da ke karamar Hukumar Tudun Wada a Jihar Kano a ranar 14 ga Fabrairun bana, jim kadan bayan an kai hari a ofishin ’yan sanda na Kibiya.
Tambari Yabo ya ce jami’ansu biyar da kuma wani mai taimaka musu ana yi musu tuhuma ta cikin gida kan sakacin da suka yi aka kashe Farfesa Falaki a gabansu. Yabo wanda tsohon Sufeto Janar ya umarta ya biniciki lamarin ya ce mutanen kauyen biyar da aka kama kan zargin kisan an gurfanar da su gaban kotu bisa tuhumar kisan kai.