Kotu ta sallami kananan yara da ake zargi da cin amanar kasa

Kotu ta kori karar da ake zargin kananan yara da cin amanar kasa a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya.

Kotu ta sallami kananan yara da ake zargi da cin amanar kasa

Kotu ta kori karar da ake zargin kananan yara da cin amanar kasa da neman kifar da gwamanti a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya.

A safiyar Talata Mai Shari’a  Obiora Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ya yi watsi da karar bayan a ranar Juma’a ta bayar da yaran su 119 da ake zargi beli a kan Naira miliyan 10 kowannensu.

Ya yi hakan ne bayan bukatar janye kara da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya gabatar, ta hannun lauyansa, Mohammed Abubakar.

Lauyan ya shaida wa kotun cewa Gwamnatin Tarayya ta karbe ragamar gabatar da karan, kuma ta yanke shawarar janye karar ‘yan kasa da shekara 18 daga cikin wadanda ake zargi kan zanga-zangar.

Zaman kotun na zuwa na sa’o’i bayan Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ba da umarnin sakin yaran wanda suka shafe kusan kwana 100 a tsare.

Aminiya ta ruwaito yadda hudu daga cikin yara 76 daga cikinsu suka yanke jiki suka fadi a cikin kotu a lokacin da ake gurnfanar da su ranar Juma’a.

Wanann lamari ya sa alkalin dakatar da zaman na tsawon minti 40 kafin daga bisani a ci gaba, inda a karshe wadanda ake zargin suka ki amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa.

Tun a watan Agusta yaran suke tsare inda Gwamantin Tarayya ke zarginsu da cin amanar kasa, da yunkurin kifar da gwamanti bayan an kama su da tutar kasar Rasha a lokacin zanga-zangar yunwa a jihohin Kano da Kaduna da Bauchi da sauransu.

Abin da ya faru a kotun ya jawo wa gwamanti suka, da lauyoyi da malaman addini da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty Interanational da manyan ’yan siyasa, musamman ganin cewa yaran su sama da 76 ba su kai shekara 18 da haihuwa ba.

Daga bisani Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, ya karbe ragamar lamarin, bayan da ya umarni ’yan sanda su mika masa fayil din tuhume-tuhumen.

A ranar Litinin Tinubu ya ba da umarnin gaggauta sakinsu, tare da gudanar da bincike da hukunta masu hannu wannan danyen aiki.

Sai dai duk da haka, malaman addini da lauyoyi irin su Femi Falana (SAN) da sauran masu fafutukar kare hakkin dan Adam suna kira da a biya yaran diyya tare hukunta duk masu hannu a badakalar.