Kotu ta sallami kwarori 4 da ake zargi da tara makamai a Kano
Wata Babbar Kotun Majistare da ke Karu a yankin Birnin Tarayya, Abuja ta sallami mutanen Lebanon hudu da aka kama bisa zargin suna da hannu a makaman da aka kama a Kano da kuma wasu ayyukan ta’addanci a Kano da Abuja.Alkalin Kotun Majistare Muyiwa Oyeyepo ya yi watsi da karar bayan da Hukumar Tsaron Cikin […]
Wata Babbar Kotun Majistare da ke Karu a yankin Birnin Tarayya, Abuja ta sallami mutanen Lebanon hudu da aka kama bisa zargin suna da hannu a makaman da aka kama a Kano da kuma wasu ayyukan ta’addanci a Kano da Abuja.
Alkalin Kotun Majistare Muyiwa Oyeyepo ya yi watsi da karar bayan da Hukumar Tsaron Cikin Gida (SSS) ta janye tuhumar da ake yi ga abokin mallaka na Shagon Amigo Supermarket da ke Abuja, Mustapha Darwish Fawaz da Talal Roda da Abdullah Tahini da Hussain Nurudeen Kossdi.
Lauyan Hukumar SSS, Cliff Osagie ya shaida wa kotun a shekaranjiya Laraba cewa, Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar ta janye tuhumar da take yi ga mutanen saboda laifin ta’addanci ya tsallake hurumin kotun.
Lauyan kariya Ahmed Raji bai nuna adawa da bukatar ba.
Bayanin farko na gabatar da karar wanda a kansa ne aka tura su zaman jiran shari’a a ranar 5 ga Yuni, ya ba da karfi ne wajen zargin hada baki da shigo da makamai don aikata ta’addanci, wanda hakan ya saba wa sashi na 97 na kundin laifuffuka da hukuncinsu (Final Kod) da kuma dokar Yaki da Ta’addanci ta shekarar 2011.
An kama wadanda ake zargin ne a mamaya biyu da rundunar hadin gwiwa (JTF) da jami’an Hukumar SSS suka kai a gida mai Lamba 3, Titin Gaya a Bompai, Kano da kuma kantin Amigo Supermarket da ke Wuse 2 Abuja a makon jiya, inda aka gano makamai da harsasai da dama.
Wani jami’in Hukumar SSS ya ce za a ci gaba da tsare wadanda ake tuhumar a hannun hukumarsu har zuwa lokacin da za a kammala bincike tare da samun umarni na gaba.