Kotu ta sanya 22 ga Yuli don kammala sauraron shari’ar takarar Sanatan APC a Gombe
Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed ta ɗage shari’ar zuwa 22 ga watan Yuli, 2026.
Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta ɗage shari’ar da ke ƙalubalantar zaɓen fid-da-gwani na jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Gombe ta Kudu zuwa 22 ga watan Yuli, 2026, domin karɓar jawabai na ƙarshe daga ɓangarorin da ke cikin shari’ar.
Shari’ar na gaban Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed, bayan Hon. Bilyaminu Babadidi ya shigar da ƙara a kan jam’iyyar APC, Jerry Joseph Damara da kuma INEC.
- An ceto wani yaro da aka sace, an kama mutum 4 Gombe
- Mutum 18 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Neja
Babadidi na ƙalubalantar ayyana Jerry Joseph Damara a matsayin ɗan takarar APC na kujerar Sanatan Gombe ta Kudu.
A zaman kotun, lauyan mai ƙara ya gabatar da shaidu huɗu, ciki har da Babadidi, tare da miƙa wasu takardu a matsayin hujjoji.
Shaidun sun ce ba a gudanar da zaɓen fid-da-gwani ba a rumfunan zaɓe, ƙananan hukumomi.
Sun kuma ce ba a tura jami’an zaɓe ko kayan gudanar da zaɓen ba.
Haka kuma, sun bayyana cewa mai ƙarar ya kai ƙorafi ga Kwamitin Ɗaukaka Ƙara na APC, amma ba a ɗauki wani mataki kan ƙorafin nasa ba.
A ɓangaren masu kare kansu, jam’iyyar APC ta gabatar da shaida guda ɗaya, Rabilu Musa, wanda ya ce shi ne shugaban Kwamitin Zaɓen APC daga hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa.
Ya shaida wa kotu cewa an gudanar da zaɓen fidda gwani na APC a Gombe, ciki har da mazabar Sanatan Gombe ta Kudu, a ranar 18 ga watan Mayu, 2026.
Sai dai yayin da ake masa tambayoyi, ya amince cewa ba a gabatar da kundin sunayen masu kaɗa ƙuri’a a matsayin hujja a gaban kotu ba.
Bayan kammala gabatar da shaidu da hujjoji daga dukkan ɓangarorin, Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed ta ɗage shari’ar zuwa 22 ga watan Yuli, 2026, domin karɓar jawabai na ƙarshe kafin yanke hukunci.