Kotu ta sauke Shugaban PDP daga muqaminsa
Wata Babbar Kotu a Abuja ta sauke Shugaban riko na Jam’iyyar PDP na riko, Uche Secondus, daga kan mukaminsa.Kotun ta yanke hukuncin ne ranar Talata bayan wadansu ’ya’yan jam’iyyar a karkashin jagorancin tsohon Mai bai wa Shugaban kasar Shawara kan Harkokin Siyasa, Ahmed Gulak, suka kai shi kara, inda suka bukaci a sauke shi saboda […]
Wata Babbar Kotu a Abuja ta sauke Shugaban riko na Jam’iyyar PDP na riko, Uche Secondus, daga kan mukaminsa.
Kotun ta yanke hukuncin ne ranar Talata bayan wadansu ’ya’yan jam’iyyar a karkashin jagorancin tsohon Mai bai wa Shugaban kasar Shawara kan Harkokin Siyasa, Ahmed Gulak, suka kai shi kara, inda suka bukaci a sauke shi saboda ya fito ne daga yankin Kudu, sabanin kundin tsarin mulkin jam’iyyar da ya ce dan yankin Arewa ne ya kamata ya zama shugaban jam’iyyar.
Alkalin Kotun Huseini Baba-Yusuf ya ce Mista Secondus yana kan kujerar shugabancin jam’iyyar ne ba bisa ka’ida ba. Ko Sai dai Mista Secondus wanda ya fito daga Jihar Ribas wadda take yankin Kudu-maso-Kudu, ya ce zai daukaka kara.
Rikicin shugabancin jam’iyyar ya barke ne bayan saukar da shugabanta Adamu Mu’azu, wanda ya fito daga Jihar Bauchi wadda take yankin Arewa, ya yi daga mulki, sai aka bai wa Secondus rikon kwarya, lamarin da Alhaji Gulak ya ce ya saba wa dokar jam’iyyar.
Har ila yau, jam’iyyar na ci gaba da fama da rikice-rikice tun bayan da ta sha kaye a hannun Jam’iyyar APC a babban zaben bana.