Kotu ta soke belin da ta bai wa Dokta Dutsen Tanshi

Kotu za ta iya bai wa jami’an tsaro umarnin kama shi a kowane lokaci.

Kotu ta soke belin da ta bai wa Dokta Dutsen Tanshi

Dokta Idris Dutsen Tanshi

Kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Bauchi ta soke belin da ta bayar kan malamin nan na addinin Islama, Dokta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi.

Wannan dai na zuwa ne bayan kotun ta mayar wa da waɗanda suka tsaya wa malamin takardun kadarorinsu da suka bayar domin karɓar belin shi da ta bayar a baya.

Hakan dai na nufin a kowanne lokaci za a iya kama shi kamar yadda lauyansa, Barista Ahmad Musa Umar ya shaida wa BBC.

A cewar Barista Ahmad, “kotu za ta iya bai wa ’yan sanda takardar kama Dokta Idris a kowanne lokaci.”

“Kotun ta ce ta ɗage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan nan na Janairu, wanda kuma take tsammanin jami’an tsaro su kai mata shi gabanin wannan rana,” in ji Barista Ahmad Musa.

Ana dai tuhumar Dokta Idris ne da laifuka biyu da suka haɗa da kalaman batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W, sai kuma laifin tayar da zaune tsaye.

Har yanzu dai ba a fara sauraron wannan shari’a ba kan waɗannan tuhume-tuhume.

Amma a baya ya yi zaman gidan kaso kan waɗannan tuhume-tuhume na tsawon kwana 39 tsakanin watan Yuni da Yuli, in ji lauyansa.

Aminiya ta ruwaito cewa, tun a watan Mayun bara ne Kungiyar Fityanul Islam ce ta maka malamin a Kotun Majistare da ke Jihar Bauchi, bisa zargin sa da kalaman batannci ga Manzon Allah (SAW), zargin da malamin ya musanta.

’Yan sanda sun gurfanar da Sheikh Idris Dutsen Tanshi bisa zargin tayar da hankulan jama’a.

A kwanakin baya ne wadansu kungiyoyin addini guda 17 karkashin kungiyar Fityanul Islam, ta rubuta takardar koke ga kwamishinan ’yan sandan jihar, bisa zargin Malamin ya yi batanci ga Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi).

Lamarin da ya sanya ke nan ’yan sanda gayyatar dukkan bangarorin da abin ya shafa inda Dokta Abdulaziz, wanda shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi, ya amsa gayyatar ’yan sandan kafin daga bisani aka gurfanar da shi a gaban kotu kan wannan zargi.

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya

Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka