Kotu ta soke laifin ta’addanci kan wanda ake zargi da tada bom a Nyanya
Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta soke karar laifin ta’addanci da Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya ya shigar a kan Sadik Ogwuche, wanda aka yi zargin dan Boko Haram ne da ya jagoranci tada bom a unguwar Nyanya kwanakin baya.A yayin da yake yanke hukuncin soke karar, Mai shari’a Adeniyi Ademola ya bayyana […]
Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta soke karar laifin ta’addanci da Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya ya shigar a kan Sadik Ogwuche, wanda aka yi zargin dan Boko Haram ne da ya jagoranci tada bom a unguwar Nyanya kwanakin baya.
A yayin da yake yanke hukuncin soke karar, Mai shari’a Adeniyi Ademola ya bayyana cewa ya soke karar ce saboda rashin tabbatar da hujjoji kwarara daga bangaren ’yan sanda.
A wani zama da kotun ta yi a baya, lauyan Sadik ya koka da cewa an hana wanda ake tuhumar ya gana da iyalinsa da ’yan uwansa da lauyansa da ma likitansa. Ya kuma ce ya samu rashin lafiya a sanadiyyar tsare shi da aka yi ba tare da an gabatar da shi gaban shari’a ba. A nan ne mai shari’ar ya ba da umurnin da a bar lauyoyi uku, da matarsa da dan uwansa daya su rika ganawa da shi.
Lauyan masu shigar da kara, Cliff Osagie ya sanar da kotun cewa Antoni Janar na Tarayya zai amshi kadin karar, inda su za su ci gaba da tsare wanda ake tuhuma.
Ogwuche, dan shekara 29 dai soja ne da ya tsere daga wurin aiki. Shi ne aka yi zargin ya jagoranci kai harin bam a ranar 14 ga watan Afirilun bana, a tashar motar Nyanya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa kuma ya lalata motoci. Daga bisani ne ’yan sanda suka gano shi a Sudan, inda aka dawo da shi Najeriya a ranar 15 ga Yulin da ya gabata.
Mai shari’a dai ya daga shari’ar zuwa 5 ga Disamba, domin ci gaba da sauraren shari’ar, inda za a duba yiwuwar bayar da shi beli.