Kotu ta soke tsige Nyako
Wata Kotun daukaka kara da ke Yola ta soke tsige tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako, wanda wakilan Majalisar Adamawa 17 daga cikin 25 suka tsige a ranar 15 ga Yulin shekarar 2014, bayan sun amince da rahoton wani kwamiti da suka kafa don bincikarsa game da zargin almundahana.Rahoton dai ya samu Nyako da […]
Wata Kotun daukaka kara da ke Yola ta soke tsige tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako, wanda wakilan Majalisar Adamawa 17 daga cikin 25 suka tsige a ranar 15 ga Yulin shekarar 2014, bayan sun amince da rahoton wani kwamiti da suka kafa don bincikarsa game da zargin almundahana.
Rahoton dai ya samu Nyako da laifi kan zarge-zarge 16 da suka shafi aikata ba daidai ba.
Sai dai a hukuncin da Kotun daukaka karar ta yanke a jiya Alhamis ta ce, tsige Murtala Nyako a matsayin Gwamnan Jihar Adamawa a shekarar 2014 ya saba wa tanadin doka.
Hukuncin da Mai shari’a Tunde Ayotoye ya karanta ya ce, dukkan alkalan kotun sun amince cewa ba a ba Nyako damar kare kansa ba a yayin zaman majalisar. Alkalan sun ce an tauye ’yancin tsohon Gwamnan, don haka suka bayyana hanyar da aka bi wajen tsige shi a matsayin batacciya kuma an rusa ta.
Kotun ta bayar da umarnin a ba wa Nyako duk wasu hakkokinsa na sauran zangonsa na Gwamna kuma a biya shi dukkan hakkokinsa har zuwa lokacin da wa’adin mulkinsa ya zo karshe.
Sai dai kotun ta yi watsi da bukatar Nyako ta a mayar da shi kan kujerarsa ta Gwamnan Jihar. Alkalan sun ce wa’adin mulkinsa ya riga ya kare. Kotun ta soki “nuna gadara da girman kai” na Majalisar Dokoki ta Jihar Adamawa da wasu ’ya’yanta kan wannan lamari.