Kotu ta soke ’yan takarar APC 16 na Majalisar Dokokin Ribas
Da wannan hukunci, APC ta rasa rabin ’yan takararta na Majalisar Dokokin Jihar Ribas
Babbar Kotun Tarayya ta soke ’yan takarar Jam’iyyar APC a mazabu 16 na Majalisar Dokokin Jihar Ribas.
Kotun da ke zamanta a Fatakwal, hedikwatar jihar, ta soke ’yan takarar APC cne saboda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ba ta sa ido a zaben ’yan takarar da jam’iyyar ta gudanar a mazabun ba.
- Na yi asarar buhu 700 na shinkafa a ambaliya —Manomi
- Sauyin Yanayi: Kasashen Turai munafukai ne —Buhari
Jam’iyyar PDP mai mulkin jihar ce ta shigar da karar kan saba wannan ka’ida wajen gudanar da zaben ’yan takarar na APC.
Da wannan hukunci, APC ta rasa rabin ’yan takararta na Majalisar Dokokin Jihar Ribas, — za ta yi takara ne a mazabu 16 a zaben 2023.
Kakakin APC na Jihar Ribas, Sogbeye Eli, ya bayyana mamaki bisa hukuncin kotun, yana cewa INEC ta gabatar wa kotu hujjoji cewa ta sanya ido a zaben ’yan takarar a mazabun da hukuncin ya shafa.
Ya ce INEC ta tabbatar da haka ne a shaidar da ta gabatar a gaban wata kotun tarayya kan karar da ke kalubalantar cancantar ’yan takarar sanata da Majalisar Tarayya na jam’iyyar ba.
Amma ya ce jam’iyyar za ta iya daukaka kara.