Kotu ta soke zaben fid-da gwanin APC na Gwamnan Taraba

Kotun ta ba da umarnin sake zaben fid-da gwanin

Kotu ta soke zaben fid-da gwanin APC na Gwamnan Taraba

Dakataccen dan Takara Gwamnan APC a Taraba Emmanuel Bwacha

Babbar Kotun Tarayya da ke Jalingo babban birnin jihar Taraba, ta dakatar da Emmanuel Bwacha, daga matsayinsa na halastaccen dan takarar Gwamnan jam’iyyar a jihar.

Kotun ta kuma ba da umarnin sake zaben fid-da gwanin Gwamnan gaba daya.

Wannan dai na zuwa ne bayan karar da guda daga ’yan takarar Gwamnan, David Sabo Kente, ya shigar gaban kotun, yana ikirarin ba a gudanar da zaben a kan ka’ida ba.

Alkalin kotun, Simon Amobede, ne ya ba da umarnin sake zaben fid-da gwanin nan da makonni biyu, tare da ba Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) umarnin daina ambato Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar Gwamnan jam’iyyar.

Haka kuma ya ce ba zai yiwu duk sakamakon zaben ya kasance da rubutu iri daya ba, bayan baturen zabe a hedkwatar rundunar ‘yan sandan Taraban ya ce ba a gudanar da zaben fid-da gwani ba a jihar sakamakon barazanar tsaro.

Alkali Amobede ya ce bayyana sakamakon zaben bogin kafin tashin jirgin sama mai zaman kansa a filin jirgin Danbaba Suntai da ke jihar da Baturen zaben yayi, bai dace ba ko kadan.

Da suke mayar da martani kan hukuncin, lauyoyin jam’iyyar APC da korarren dan takarar sun bayyana cewa za su yi nazari kan hukuncin kafin zuwa kotun daukaka kara, ko kuma shirya sabon zaben fidda gwani.