Kotu ta soke zaben Gwamnan Bayelsa

Kotun ta ba da umarnin sake zabe nan kwana 90

Kotu ta soke zaben Gwamnan Bayelsa

Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri

Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Jihar Bayelsa da ke zama a Abuja ta soke zaben Gwamnan Jihar Bayelsa, Duoye Diri, da mataimakinsa, Lawrence Ewhrudjakpo.

Kotun mai alkalai uku a karkashin jagorancin Mai Shari’a Ibrahim Sirajo ta soke zaben ne bayan amincewa da korafin Jam’iyyar ANDP na cewa ba a sanya ta a zaben da aka yi a 16 ga Nuwamban bara ba.

Tuni kotun ta ba da umarni a sake zaben cikin kwanaki 90 masu zuwa.