Kotu ta soke zaben Gwamnan Ribas

Kotun daukaka kara ta Abuja ta tabbatar da soke zaben Gwamnan Jihar  Ribas, Nyesom Wike. Kotun a zamanta a Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun zabe ta Jihar Ribas da ta soke zaben Gwamnan. A hukunci da kotun ta yanke mai shafi 110, karkashin jagorancin Mai shari’a M.B. Dongban Mensem, ta tabbatar da cewa Gwamna […]

Kotu ta soke zaben Gwamnan Ribas
Kotu ta soke zaben Gwamnan Ribas

Kotun daukaka kara ta Abuja ta tabbatar da soke zaben Gwamnan Jihar  Ribas, Nyesom Wike. Kotun a zamanta a Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun zabe ta Jihar Ribas da ta soke zaben Gwamnan.
A hukunci da kotun ta yanke mai shafi 110, karkashin jagorancin Mai shari’a M.B. Dongban Mensem, ta tabbatar da cewa Gwamna Wike bai cika ka’idojin da dokar zabe ta tanada ba. Don haka kotun ta bayar da izinin sake gudanar da zabe nan  da kwana 90.
Idan ba a manta ba, a makonnin da suka wuce ne kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar ta ce ba a cika ka’idojin zabe ba, wajen zaben Gwamnan Ribas.
Yanzu dai Gwamna Wike ya nufi  Kotun koli, inda zai bukaci kotun ta yi watsi da karar da dan takarar Jam’iyyar APC Dakuku Pterside ya kai game da zaben  na 11 ga Afrilu bana, inda ya yi zargin an tafka magudi.