Kotu ta soke zaben Kakakin Majalisar Dokokin Filato

Kotun ta ce ’yan takarar PDP ne suka lashe kujerun

Kotu ta soke zaben Kakakin Majalisar Dokokin Filato

Kotun sauraron karrakin zaben ’yan majalisa da ke zamanta a Jos, Jihar Filato a ranar Juma’a ta soke zaben Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Moses Sule.

Kakakin, wanda dan jam’iyyar PDP ne an soke zaben nasa ne tare da Danjuma Azi, dan majalisa mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa a majalisar.

Kotun dai ta ayyana tsohon Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Naanlong Daniel da Mark Na’ah, ’yan jam’iyyar APC a matsayin halastattun wadanda suka lashe zaben na ranar 18 ga watan Maris.

Masu karar dai sun shigar da ita ne suna kalubalantar zabukan saboda da’awar da suka yi cewa PDP ba ta ma cancanta ta shiga zaben ba.

Da yake zartar da hukuncin, jagoran alkalan, Mai Shari’a Muhammad Tukur, ya ce PDP ba ta cancanta ta tsayar da ’yan takarar ba a zaɓen.

Ya ce jam’iyyar ba ta da shugabanci, “saboda haka babu ba za ta tsayar da babu ba.”

Kotun ta kuma ce PDP ta ki bin umarnin hukuncin Mai Shari’a S.P. Gang na Babbar Kotun Jihar Filato da ya yanke a ranar 26 ga watan Nuwamban 2020, wanda ya umarci jam’iyyar ta gudanar da tarukanta a matakan mazaba.

Ko a ranar Alhamis dai sai da kotun ta soke kujerun ’yan majalisar su biyu na jam’iyyar ta PDP.

Tags