Kotu ta soke zaben Sanatan APC a Kogi, ta ce ’yar takarar PDP ce ta lashe
Kotun ta ce Natasha ta PDP ce ta lashe zaben
Kotun sauraron kararrakin zaben ’yan majalisa a Jihar Kogi ta soke zaben kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya, Abubakar Ohere.
Kotun ta kuma ayyana Natasha Akpoti-Uduagan ta jam’iyyar PDP a matsayin wacce ta lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata.
- Kotu ta tabbatar da nasarar Kofa a matsayin dan majalisar tarayya
- An yi karin kudin mitar lantarki zuwa N81,000
Da take yanke hukunci, kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a K.A. Orjiako, ya ce an kara adadin yawan kuri’un da Ohere ya samu a akwati mai lamba 9 da ke Karamar Hukumar Ajaokuta.
Ya kuma ce jami’in hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ya rage kuri’un da PDP ta samu a mazabar yayin tattara sakamakon.
Alkalin ya kuma ce da gangan an ki shigar da sakamakon jam’iyyar PDP a wasu akwatina guda uku na dai waccan Karamar Hukumar.
Kotun ta ce sakamakon da Natasha ta samu a wadancan akwatinan guda 9 sun kama 1,073 ne ba 77 din da aka shigar mata ba, inda ta ce an kara wa dan takarar APC kuri’u daga 1,031 zuwa 1,553.