Kotu ta tabbatar da zaben Gwamnan Filato Simon Lalong

Kotun sauraren kararrakin zabe dake zama a garin Jos babban birnin jihar Filato, ta tabbatar da zaben gwamnan jihar Barista Simon Bako Lalong na jam’iyyar APC. Kotun ta tabbatar da zaben gwamna Lalong din ne bayan da tayi watsi da karar da dan takarar gwamnan jihar, karkashin jam’iyyar PDP Gyang Pwajok ya gabatar mata, a […]

Kotu ta tabbatar da zaben Gwamnan Filato Simon Lalong
Kotu ta tabbatar da zaben Gwamnan Filato Simon Lalong

Kotun sauraren kararrakin zabe dake zama a garin Jos babban birnin jihar Filato, ta tabbatar da zaben gwamnan jihar Barista Simon Bako Lalong na jam’iyyar APC. Kotun ta tabbatar da zaben gwamna Lalong din ne bayan da tayi watsi da karar da dan takarar gwamnan jihar, karkashin jam’iyyar PDP Gyang Pwajok ya gabatar mata, a ranar litinin din nan da ta gabata.

Da yake yanke wannan hukumci, shugaban kotun Mai shari’a Johnson Candide ya bayyana cewa kotun tayi watsi da wannan karar ne saboda masu karar sun gaza kawo hujjojin da zasu tabbatar da gaskiyar karar da suka gabatar.
Ya ce Pwajok da jam’iyyarsa ta PDP sun yi zargin cewa wai an aikata laifuffuka a lokacin zaben, amma sun kasa kawo shedun da zasu tabbatar da wannan zargi.
Mai shari’a Candide ya ce dukkan bayanin da masu karar suka gabatarwa kotun, bayanai ne na jita-jita. Don haka ya ce kotun tayi watsi da wannan kara.
Daga nan ya umarci masu karar su biya diyar naira dubu 50 ga wadanda suka kai karar.
Da yake magana kan wannan nasara da ya samu a wata sanarwa da aka raba ’yan jarida, da ke dauke da sanya hanun mai taimaka masa na musamman kan harkokin ’yan jarida Mista Mark Longyen. Gwamnan jihar ta Filato Barista Simon Lalong ya mika godiyarsa ga Allah kan wannan nasara da ya samu.
Ya ce babu shakka wannan nasara da ya samu ba tasa ba ce shi kadai, ta al’ummar jihar Filato ne gabaki daya. Domin sune suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka je masa kuri’a don ganin sun fita daga cikin mulkin danniya, da suka yi shekara 8 suna fama da shi a jihar.
Ya yi kira ga ’yan adawa da gwamnatinsa da sauran al’ummar jihar su baiwa gwamnatin jihar, goyan baya da hadin kai domin ta cimma nasara kan kudurorin da ta sanya a gaba na bunkasa jihar.