Kotu ta tabbatar da zaben Sanata Jonah Jang
Kotun Sauraron kararrakin Zaben Majalisar Tarayya da ke Jos a Jihar Filato, ta tabbatar da zaben da aka yi wa tsohon Gwamnan Jihar Jonah Jang na Jam’iyyar PDP a matsayin Sanatan Filato ta Arewa. Kotun ta tabbatarwa da zaben Sanata Jonah Jang ne bayan da ta yi watsi da karar da Misis Eunice Ayisa Sambo […]
Kotun Sauraron kararrakin Zaben Majalisar Tarayya da ke Jos a Jihar Filato, ta tabbatar da zaben da aka yi wa tsohon Gwamnan Jihar Jonah Jang na Jam’iyyar PDP a matsayin Sanatan Filato ta Arewa.
Kotun ta tabbatarwa da zaben Sanata Jonah Jang ne bayan da ta yi watsi da karar da Misis Eunice Ayisa Sambo ta Jam’iyyar APC ta shigar a zaman da ta yi a ranar Asabar da ta gabata.
Da yake yanke hukunci kan karar Shugaban Kotun Mai shari’a Lanre Akeredolu ya ce, kotun tayi watsi da karar ne bayan da mai karar ta kasa kawo hujjojin da za su sanya a soke zaben. “A wannan kara an kaso kawo hujjojin da za su gamsar da wannan kotu, don haka kotun ta yi watsi da karar. Kuma ta umarci mai karar ta biya Naira dubu 200 ga wanda aka yi karar,” inji alkalin.
Bayan yanke hukuncin lauyan Jam’iyyar PDP da Sanata Jang Mista S. Oyawole ya nuna gamsuwa da hukuncin kotun, inda ya ce, an yi wa dukkan bangarorin biyu da al’ummar mazabar Filato ta Arewa adalci.
Sai dai lauyan Jam’iyyar APC, Mista Jim Gotom ya ce za su yi nazari, kan wannan hukunci kafin su san matakin da za su dauka a gaba.
Tun da farko Misis Eunice Ayisa Sambo, ta hannun lauyanta Mista Garba Pwul ta shigar da karar ne tana kalubantar nasarar Jonah Jang a zaben, inda ta ce idan aka lissafa ainihin kuri’u na gaskiya da aka jefa a zaben, za a gano ita ce ta lashe zaben.
Kuma ta yi zargin cewa an yi amfani da kuri’u na bogi a lokacin zaben, kuma ba a yi amfani da na’urar tantance masu zabe a kananan hukumomin Jos ta Kudu da Barikin Ladi da Riyom a lokacin zaben ba, don haka mai karar ta bukaci kotun ta dawo da wanda aka ce shi ne ya lashe zaben tare da bayyana ta a matsayin wadda ta yi nasara.