Kotu ta tabbatar wa Alhassan Doguwa nasara
Kotun ta ce duk dalilai uku da mai karar ya dogara da su ba su da tushe balle makama.
Tsohon Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya yi nasara a karar da Salisu Yushau Abdullahi na jam’iyyar NNPP ya shigar a gaban kotun sauraron kararrakin zabe da ke zamanta a Kano.
Tun da farko dai Abdullahi na jam’iyyar NNPP ya roki kotun da ta soke nasarar Alhassan Doguwa a matsayin wakilin mazabar Doguwa da Tudun Wada a Majalisar Tarayya.
- Google na bikin cika shekaru 60 da haihuwar marigayi Rashidi Yekini
- Najeriya ta yi galaba kan kamfanin P&ID a shari’ar bashin dala biliyan 11
Sai dai da yake yanke hukunci kan karar da Abdullahi ya shigar a kan dan takarar na jam’iyyar APC, kwamitin alkalan mai mutum uku karkashin jagorancin mai shari’a L.B. Owolabi ya ce wanda ya shigar da karar ya gaza tabbatar da kokensa da gamsassun hujjoji kamar yadda doka ta tanada.
Mai shari’a Owolabi ya ce duk dalilai uku da mai karar ya dogara da su — da suka hada da cin hanci da rashawa da Doguwa ya yi, da rashin yi wa Dokar Zabe, da rashin samun halastattun kuri’un da ake bukata — ba su da tushe balle makama don haka ba za a yarda da su a matsayin dalilan soke zaben ba.
Dangane da zargin aukuwar tashe-tashen hankula a lokacin zabe, shaidu 21 da mai karar ya gabatar, sun ba da shaida akasin haka, inda suka bayyana cewa ba a samu wani tashin hankali ba a lokacin zaben.
Kotun, a cikin hukuncin da ta yanke, ta amince da cewa dukkan shaidu 32 da mai kara ya gabatar, sun kasa bayar da kwakkwarar hujjar da za ta tilasta a soke zaben.
Yadda Doguwa ya samu nasara a zabe
Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Afrilun da ya gabata ne Honarabul Alhassan Ado Doguwa, ya lashe zaben dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada na Jihar Kano.
Tun a shekarar 2007 Honarabul Doguwa ya shiga zauren majalisar, inda a yanzu ya zamana cewa ya lashe zaben kujerar karo na biyar a matsayin mai wakiltar kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada a matakin Tarayya.
Da yake sanar da sakamakon a Afrilun bana, Baturen Zaben Farfesa Sani Ibrahim ya bayyana cewa Doguwa ya samu kuri’u 41,573 don haka shi ne ya zama zakara.
Babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar NNPP, Air Commodore Salisu Yushau wanda yazo na biyu ya samu kuri’u 34,831.
Ana iya tuna cewa, a ranar 25 ga watan Fabrairu ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gudanar da zaben ’yan Majalisar Tarayya, inda ta ayyana zaben mazabar Doguwa/Tudun Wada a matsayin wanda bai kammala ba.
A wancan lokaci dai INEC ta ce ta yanke wannan hukunci ne sakamakon aringizon kuri’u da kuma tashe-tashen hankula da aka samu a lokacin zaben musamman a wasu daga cikin mazabun garin Tudun Wada.
Haka kuma, a lokacin da yake sanar da sakamakon zaben na watan Fabrairu, Baturen Zaben Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, ya bayyana cewa ya sanar da sakamakon zaben ne bisa tursasawa.
Wannan shi ne dalilin da INEC ta sake gudanar da zaben domin tabbatar da sahihancin sakamakonsa.
Alhassan Doguwa na daya daga cikin wadanda suka nemi takarar Kakakin Majalisar Wakilai ta 10, amma daga bisani suka janye wa Abbas Tajudeen.