Kotu ta tabbatar wa APC nasarar zaben gwamnan Benuwe

Kotun ta ce ta kori ƙarar ne saboda ba ta da hurumin sauraron batun da aka kai mata.

Kotu ta tabbatar wa APC nasarar zaben gwamnan Benuwe

Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia

Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamnan Jihar Benuwe da ke zamanta a Makurdi, ta tabbatar da nasarar Gwamna Hyacinth Alia na jam’iyyar APC a zaɓen ranar 18 ga watan Maris.

Kotun ta yi watsi da karar da ɗan takarar jam’iyyar PDP, Titus Uba, ya shigar gabanta, inda yake kalubalantar sakamakon zaɓen.

Kotun ta ce ta kori ƙarar ne saboda ba ta da hurumin sauraron batun da aka kai mata.

Tawagar alƙalan kotun uku ƙarƙashin jagorancin mai shari’a, Ibrahim Karaye, sun bayyana cewa kotun ba ta da hurumin sauraron karar ne saboda abin da aka kai mata ya shafi batutuwa ne na gabanin zaɓe kamar yadda yake a sashe na 285 na Dokar Zaɓe.

Mista Titus na zargin Mista Alia da gabatar da takardar shaidar kammala karatu ta jabu a lokacin da ya tsaya takara.

Sai dai kotun ta ce a gaban Hukumar Zaɓe ta INEC ya kamata ya kai ƙorafinsa.

Sakamakon zaɓen da INEC ta fitar a wancan lokaci, ya nuna cewa Mista Alia ya samu nasara ne da kuri’u 473,933, inda ya doke takwaransa na PDP, Titus Uba, wanda ya samu kuri’u 223,913.

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS

Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar rushe Hukumar EFCC