Kotu ta tilasta wa banki bayar da bayani kan badakalar bashi
Ga alamu tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama a zamanin mulkin Shugaban Jonathan, Stella Oduah ta fada taskun shari’a, inda Kotun Tarayya da ke Legas ta bayar da ummarni ga bankin First Bank da ya bayar da cikakkun bayanai kan bashin da ya ba hukumar sufurin da ake zargin ministar ta sayo motocin sulke. Kotun ta […]
Ga alamu tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama a zamanin mulkin Shugaban Jonathan, Stella Oduah ta fada taskun shari’a, inda Kotun Tarayya da ke Legas ta bayar da ummarni ga bankin First Bank da ya bayar da cikakkun bayanai kan bashin da ya ba hukumar sufurin da ake zargin ministar ta sayo motocin sulke.
Kotun ta bayar da ummarnin da ya tislata wa bankin bayar da dama ga kungiyar nan mai suna Enough is Enough, kungiyar da ke fafutukar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, ta samu cikakken bayanin da take so dangane da batun kamar yadda kungiyar ta nema a ranar 30 ga watan Oktoban shekarar 2013.
Alkalin kotun mai shari’a Muhammed Yunusa ya bayar da ummarnin ne a hukuncin da ya yanke sakamakon karar da kungiyar EIE ta shigar saboda bankin ya ki ya ba kungiyar cikakken bayani.
kungiyar dai ta rubuta bukatar samun bayanin ne a karkashin dokar ’yancin samun bayanai ta ranar 30 ga watan Oktoban shekarar 2013, inda ta nemi bankin First Bank ya ba ta cikakken bayani.
karar wacce kungiyar ta shigar a ranar 9 ga watan Yunin shekarar 2014 ta hannun lauyanta Mista Ayodeji Ackuah na kungiyar ’yancin samun bayanai ta lauyoyi ya zama babbar nasarar da kungiyar ta samu tun lokacin da aka kafa ta.
Hakazalika kungiya EIE ta nemi kotun da ta yanke hukunci dangane da saba doka da bankin ya yi, na hana ta samun bayanai kan batun inda ta ce matakin da bankin ya dauka ya saba wa sashi na 4 na (b) da shashi na 7 karamin sashi na (1) da sashe na 2 da na 3 na dokar ’yancin samun bayanai.
kungiyar ta taba samun irin wannan ummarnin daga wata kotu a watan Maris na shekarar 2015, inda kotu ta tilasta wa kamfanin motoci na Coscharis ya ba kungiyar cikakkun bayanai na hada-hadar kamfanin.