Kotu ta tsare dan majalisar wakilai kwana 2 kafin zabe

Wata kotun majisatre ta tsare dan Majalisar Tarayya daga  Kam’iyyar APC Ephraim Nwuzi, kwana biyu kafin zaben da yake  neman yin tazarce a kujerar.  Rundunar ’yan sandan jihar ce ta gurfanar da dan Majalisar, bisa zargin cin amanar kasa, hada baki, da tayar da rikici. Asibitocin Abuja za su fara amfani da POS Ganduje ya […]

Kotu ta tsare dan majalisar wakilai kwana 2 kafin zabe

Wata kotun majisatre ta tsare dan Majalisar Tarayya daga  Kam’iyyar APC Ephraim Nwuzi, kwana biyu kafin zaben da yake  neman yin tazarce a kujerar. 

Rundunar ’yan sandan jihar ce ta gurfanar da dan Majalisar, bisa zargin cin amanar kasa, hada baki, da tayar da rikici.

A zaman kotun na ranar Laraba, lauyan wanda ake zargi Emenike Ebete ya nemi beli, sai dai masu kara da ’yan sandan da ke binciken lamarin sun soki hakan.

Bayan sauraron duka bangarorin, alkalin kotun, O Amadi Nna ya sa a tsare da Majalisar zuwa ranar 3 ga watan Maris, lokacin da gwamnati za ta fitar da tuhumar da take masa.

Baya an kammala zaman kotun ne kuma lauyansa ya bayyana wa manema labari cewa laifin da aka zargi dan majalisar da shi bai kai a tsare shi ba.

A safiyar ranar Laraba ne dai ’yan sanda suka kamo dan majalisar a gidansa da ke Karamar Hukumar Etche, bayan gayyatarsa da suka taba yi kan wani bidiyo da a ciki yake umartar magoya bayansa su far wa mutane a lokutan zabe, ciki har da ma’aikatan Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).