Kotu ta tsare dan sanda a kurkuku kan damfarar N128m

Kotu ta tisa keyar wani hafsan dan sanda zuwa gidan yari kan zargin yi wa wani dan kasuwa damfara ta tsabar kudi Naira miliyan 128

Kotu ta tsare dan sanda a kurkuku kan damfarar N128m

Kotu ta tisa keyar wani hafsan dan sanda zuwa gidan yari kan zargin sa da yin damfara ta kudi Naira miliyan 128.

An gurfanar dan sandan mai suna DSP Jerry Ogunsakin ne a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, bisa zargin sa da hada baki da kuma damfarar wani dan kasuwa kudi Naira miliyan 128.

Dan sanda mai gabatar da kara, Chukwu Agwu, ya shaida wa kotun cewa DSP Jerry tare da wasu mutum biyar ne suka yaudari dan kasuwar da ke neman canjin Dala, cewa su ’yan canji ne kuma suna da Dala ta Naira miliyan 128 da yake bukata.

Sai dai kuma bayan dan kasuwar ya tura musu kudin a watan Nuwambar 2022, sai suka yi layar zana ba tare da sun ba shi ko Dala daya ba.

Sauran mutum biyar din dai sun tsere, har yanzu babu duriyarsu, amma shi dan sandan da aka gurfanar ya musanta zargin da ake masa.

A kan haka ne kotu ta ba da umarnin a tsare mata shi a gidan yari, sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Yuni da muke ciki.

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro