Kotu ta tsare dan Shahrukh Khan kan miyagun kwayoyi
An yi kwanaki ana bincike kan hannun Aryan Khan a harkar kwayoyi a Mumbai.
Kotu ta tsare Aryan, dan tauraron fina-finan Bollywood na kasar Indiya, Shahrukh Khan, kan zargin harkar miyagun kwayoyi.
Kotun da ke zamanta a birnin Mumbai ta ba da umarnin tsare dan na Shahrukh Khan tare da wasu mutum bakwai ne na tsawon kwana 14 saboda wani bincike kan hadahadar miyagun kwayoyi.
A ranar 3 ga watan Oktoba, 2021, ne ’yan sanda suka kama wasu miyagun kwayoyi a wani samame da suka kai a cikin wani jirgin ruwa a gabar tekun Mumbai.
Lauyan mai kare Aryan Khan, Satish Maneshinde, ya shaida wa kotun a madadin Aryan, cewa “A kofar shiga wurin aka tsare ni.
“Ni ba wanda na kai wa kara. Abin da na sani kawai shi ne a ranar farko na amince cewa zan kara dawowa, zatona shi ne za a samu wani ci gaba. Amma in banda karin wasu mutane da aka kama babu wani sabon abu.
“A tsawon binciken da ake min, an mayar da hanakli ne kawai a kan zamana a kasar waje. Ba a tambaye ni game da wani abu ba kuma.
“Idan har da gaske maganar da na yi ne dalilin tsare mutanen, to ya kamata shugabannin masu gudanar da binciken su fahimci ko ina da alaka da wadanda aka tsare, amma ba abin da aka yi.
“A lokacin da suka tsare Kumar, ya makata su bincika ko yana da wata laka ko dangantaka da Aryan, amma ba su yi ba.
“Wani abu kuma shi ne an tsare mutanen da suka kawo jirgin ruwan, da kuma wani dan kasar waje wanda ni ba ni da wata alaka da shi.”
Kafar yada labarai ta CNN da ta kawo labarin ta ce duk kokakin yin magana da Shahrukh Khan, ko kakakinsa, abin ya gagara.