Kotu ta tsare dillalai biyu kan zargin cin amana da cuta a Jigawa

’Yan sanda a Jihar Jigawa sun gurfanar da wadansu mutum biyu a gaban Kotun Shari’a da ke Dutse bisa zarginsu da laifin hada baki da cuta ta hanyar sayar wa wani mutum fili kuma suka sake zagayawa suka sayar da filin ga wadansu suka bar shi ba fili ba takardunsa.’Yan sandan suna tuhumar dillali Abba […]

Kotu ta tsare dillalai biyu kan zargin cin amana da cuta a Jigawa
Kotu ta tsare dillalai biyu kan zargin cin amana da cuta a Jigawa

’Yan sanda a Jihar Jigawa sun gurfanar da wadansu mutum biyu a gaban Kotun Shari’a da ke Dutse bisa zarginsu da laifin hada baki da cuta ta hanyar sayar wa wani mutum fili kuma suka sake zagayawa suka sayar da filin ga wadansu suka bar shi ba fili ba takardunsa.
’Yan sandan suna tuhumar dillali Abba Abbas da Muhammad Shitu mazauna Unguwar danmasara da Unguwar 744 Mobile da ke Dutse ne da laifin sayar wa wani mai suna Umar Ya’u fili wanda ya saya wa kanensa Adamu Ya’u a kan Naira dubu 200, amma suka ki nuna masa filin kuma suka hana shi takardun filin sannan suka rabe kudin a tsakanin junansu.
Ganin haka ne Malam Umar Ya’u ya kai karar dillalan ga ’yan sanda domin neman hakkinsa, inda su kuma suka gurfanar da su a gaban alkali domin fuskantar shari’ar.
Lokacin da Malam Umar Ya’u yake karin bayani a kotun ya ce kusan wata shida da sayen filin amma dillalan suna ta yi masa yawo da hankali babu kudin kuma sun ki nuna masa filin, wannan ne ya sa ya yi kararsu domin neman hakkin dan uwansa.
Alkalin kotun Mai shari’a Muhammad Adamu ya ingiza keyarsu dillalan zuwa gidan yari domin zaman wakafi na mako daya saboda ba a samu wanda ya amshe belinsu ba. Alkalin ya kafa hujja da sashi na 122, karamin sashi na 177 na kundin sharia na dokokin Jihar Jigawa kan manyan laifufuka wajen tsare wadanda ake tuhumar. Ya ce duk da girman laifinsu sashi na 298 na dokar ya ba da damar a ba da belinsu in sun sami wanda ya tsaya musu, kuma abin da ake zarginsu da shi ya saba wa sashi 139 na kundin manyan laifuffuka na jihar.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe