Kotu ta tsare hedmasta da mataimakinsa kan zargin yi wa dalibansu hudu fyade
A ranar Alhamis din makon jiya ne Babbar Kotun Majistare ta Hudu da ke Katsina ta bayar da umarnin tsare shugaban makarantar firamare ta Ganuwa da ke karamar Hukumar Charanci a Jihar Katsina mai suna Abubakar Isyaku (Kwade) mai shekara 56 da Mataimakinsa Abdullahi Liman (Baban Ummi) a gidan maza zuwa 6 ga Agusta bisa […]
A ranar Alhamis din makon jiya ne Babbar Kotun Majistare ta Hudu da ke Katsina ta bayar da umarnin tsare shugaban makarantar firamare ta Ganuwa da ke karamar Hukumar Charanci a Jihar Katsina mai suna Abubakar Isyaku (Kwade) mai shekara 56 da Mataimakinsa Abdullahi Liman (Baban Ummi) a gidan maza zuwa 6 ga Agusta bisa zarginsu da yin fyade ga daliban makarantarsu.
Kotun a karkashin jagorancin Mai shari’a Hadiza Muhammad danja ta bayar da umarni ne bayan sauraren karar da Saje Adamu Isa ya gabatar a gabanta inda ake tuhumar shugaban da mataimakinsa da yi wa dalibansu hudu fyade wadanda dukkansu ’yan gida daya ne.
Saje Adamu ya ce, a wani lokaci ne mahaifin yaran mai suna Dikko Umar ya kai koken faruwar lamarin a ofishin ’yan sanda da ke garin Charanci inda ya yi zargin shugaban makarantar da mataimakinsa da bata masa ’ya’ya ta hanyar yi musu fyade. Yaran abin ya shafa da aka sakaya sunansu suna tsakanin shekara hudu zuwa bakwai ne.
Mai gabatar da karar ya ce, mahaifiyar yaran ce ta lura da yadda suke gudanar da harkokinsu ba yadda ta saba ganinsu ba, inda bayan matsa musu da tambayoyi suka shaida mata cewa Malam Abubakar da Malam Abdullahi ne bayan sun ba su tsoro, suke kai su ofishin shi shugaban makarantar inda suke amfani da reza su yanyanka musu wanduna sannan su yi amfani da su daya bayan daya, daga bisani suka rika sanya musu yatsu a cikin matancinsu. Kuma bayan sun gama su gargade su cewa kada su sake su gaya wa iyayensu, in kuwa suka fadi za su gamu da su.
Saje Adamu ya ce, an kai yaran Babban Asibitin Kankiya don yi musu jinya kan raunukan da suka a matancinsu. Kuma ya ce, aikata hakan ya saba wa sashi na 96 da na 283 na kundin laifuffuka da hukunce-hukuncensu.
Mai shari’a Hadiza danja ta shaida wa wadanda ake tuhumar cewa, kotunta ba za ta tambaye su a kan cewa ko sun aikata wancan laifi da ake tuhumarsu ba ko a’a ba, saboda rashin hurumin yin haka daga kotun.
An kawo su ne domin ambaci karar a kan abin da ake tuhumarsu kawai, saboda haka sai ta dage lokacin sake ambaton karar zuwa 6 ga Agusta mai zuwa.