Kotu ta tsare lebura da laifin kisa da wuka

Kotun majistare a Kano ta tsare wani lebura dan shekara 36 Sani Musa a gidan yari saboda laifin dabawa Musa Ashiru wuka wanda ya yi sanadiyyar rasuwarsa. Musa wanda yake zaune a rukunin gidajen Rijiyar Lemo, kotun na zargin mutumin ne da laifin kisan kai yayin da Musa ya musanta zargin aikata laifin. Alkalin kotun […]

Kotu ta tsare lebura da laifin kisa da wuka

Kotun majistare a Kano ta tsare wani lebura dan shekara 36 Sani Musa a gidan yari saboda laifin dabawa Musa Ashiru wuka wanda ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

Musa wanda yake zaune a rukunin gidajen Rijiyar Lemo, kotun na zargin mutumin ne da laifin kisan kai yayin da Musa ya musanta zargin aikata laifin.

Alkalin kotun Majistarin Muhammad Jibril ne ya bayar da umarnin tsare Musa a gidan yari har zuwa lokacin da aka kammala binciken lamarin.

An dai dage sauraran shari’ar zuwa ranar 5 ga Nuwamba 2018.