Kotu ta tsare malamin makaranta kan yi wa ’yar wata 19 fyade
Kotun Majistare ta yankin Birnin Tarayya da ke garin Jiwa a Abuja ta ba da umarnin a tsare wani malamin makaranta kan zargi da ake yi masa na jikkata’yar shekara daya da wata bakwai a al’aurarta. Jami’in Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, Mista Dabid Kafanchan wanda ya gabatar da wanda ake zargin mai suna Sebastian Kuni […]
Kotun Majistare ta yankin Birnin Tarayya da ke garin Jiwa a Abuja ta ba da umarnin a tsare wani malamin makaranta kan zargi da ake yi masa na jikkata’yar shekara daya da wata bakwai a al’aurarta. Jami’in Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, Mista Dabid Kafanchan wanda ya gabatar da wanda ake zargin mai suna Sebastian Kuni mai shekara 28 da ke koyarwa a garin Karmo, Abuja a ranar Larabar makon jiya, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya dauki yarinyar ne zuwa cikin dakinsa da ke gida guda da na iyayenta, sannan ya sanya yatsarsa cikin al’aurarta inda ya kai ga yi mata rauni, ya ce aikata hakan laifi ne a doka ta 285 na dokokin Final Kod.
Jami’in ya ce, lamarin wanda ya faru a ranar 22 ga watan Mayu, an sanar wa ofishin ’yan sanda na garin al’amarin kuma daga can ne aka kai yarinyar zuwa Babban Asibitin Gwamnati na Gwarinpa, amma saboda ana yajin aiki a lokacin sai aka kai ta wani asibiti mai zaman kansa inda aka yi mata jinya. “A lokacin binciken ’yan sanda, ka amince da aikata laifin inda ka ce Shaidan ne ya sa ka aikata,” inji mai gabatar da karar.
Da alkalin kotun Mai shari’a Binta Dogon-Yaro ta waiwayi, wanda ake karar ya musanta zargin kuma ya bukaci a ba da belinsa.
Kotun ta ba da belinsa a kan Naira dubu 500 tare gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa kuma suke aiki a wata ma’aikatar gwamnati a matakin da bai gaza 16 ba, kuma suke zaune a yankin da kotun ke da hurumi. Sai ta dage ci gaba da zaman shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Yuli mai zuwa.